Kotu tayi watsi da APC, ta tabbatar da Ishaku a matsayin gwamna

Kotu tayi watsi da APC, ta tabbatar da Ishaku a matsayin gwamna

-Kotu ta tabbatar da nasara ga gwamnan jihar Taraba, Darius Ishaku

-Wannan hukuncin na kotun zaben dake Abuja ya biyo bayan hukuncin da Kotun koli ta yanke ne sakamakon amfani da shekarun karya da Danladi yayi wurin takara

-Alkalin kotun zaben ya kore kararar jam'iyyar APC da dan takarar tare da tabbatar da Ishaku a matsayin gwamna

Kotun sauraron korafin zaben gwamnan jihar Taraba wadda ke Abuja, a yau Laraba ta yi watsi da karar dan takarar APC, Abubakar Danladi ya shigar. Abubakar Danladi shi ne dan takarar gwamna na APC a zaben gwamnan da ya gabata a jihar.

Kotun tayi watsi da wannan karar ne sakamakon hukuncin da Kotun koli ta yanke a ranar 5 ga watan Yuli, inda ta tabbatar da hukunci da kotun daukaka kara ta zartar wanda ya kori karar Danaladi a bisa dalilin karyar shekarun haihuwa da yayi.

KU KARANTA:Zaben Gwamna: APC zata gudanar da zaben fidda gwani a jihohin Bayelsa da Kogi ranar 29 ga watan Agusta

A na shi hukuncin, Alkalin kotun zaben, Jastis M.O Adewarahe yace watsi da wannan karar ya zama dole, kasancewar Kotun koli ta riga ta zartar da hukunci sakamakon karyar shekaru da dan takarar APC wanda ya shigar da karar yayi.

Jam’iyyar APC da dan takarar nata, sun shigar da kara ne a kotun inda suke kalubalantar nasarar Darius Ishaku na jam’iyyar PDP a matsayin gwamnan Taraba. A cikin karar ta su, suna kalubalantar gwamnan kan cewa ba shi bane ya samu kuri’a mafi yawa a zaben da aka gudanar a jihar.

Haka zalika, daga cikin korafe-korafen APC da dan takararta akwai cewa, zaben da aka gudanar ya sabawa kundin tsarin dokokin zabe wanda aka yiwa kwaskwarima a shekarar 2010.

Tawagar alkalan wannan kotun ta zabe ne suka yi watsi da wannan kara, bayan sunyi la’akari da hukuncin Kotun koli ta kasa. A karshe dai sun yi watsi da karar kasancewar Danladi Abubakar ya yi amfani da shekarun karya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel