Ku yiwa Buhari addu’an samun nasara – Shugabannin APC sun roki yan Najeriya

Ku yiwa Buhari addu’an samun nasara – Shugabannin APC sun roki yan Najeriya

Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a karamar hukumar Lafia dake jihar Nasarawa, Alhaji Aliyu Galadima, yayi kira ga masu biyayya ga jam’iyyar da kuma yan Najeriya da su yi addu’a sannan kuma su goya ma shugaban kasa Muhammadu Buhari da sauran shuwagabanni baya don samun nasara.

Galadima ya bayyana kiran ne a ranar Talata,9 ga watan Yuli a Lafiya, a yayin ganawar da yayi tare da yan jam’iyya a yankin, inda yace akwai bukatar yin addu’o’i don shugaban kasar ya samu damar kai kasar mataki na gaba.

Ya bayyana cewa cigaba da addu’o’in zai taimaki shugaban kasa da sauran shuwagabanni wajen kawo ci gaba a kasar.

A cewar shi, kowane shugaba na bukatar goyon bayan mutanen shi wajen nasara, saboda haka ana bukatar yan Najeriya suyi addu’a da kuma goyo ma dukkanin shugabanni baya.

Ya kara da cewa jam’iyya mai mulki a kasar ta jajirce wajen samar da ingantacciyar damokardiyya ga mazauna karkara.

Shugaban har ila yau yayi kira ga mutanen yankin da yan Najeriya da su kasance masu bin doka, biyayya ga hukumomi da zama cikin kwanciyar hankali tare da juna ba tare da la’akari da banbanci ba.

Har ila yau, Mista Abdullahi Angibi (APC), mamba mai wakiltan yankin mazaban tsakiyar Lafiya a majalisan wakilai, ya bukaci mabiya jam’iyyar da su hada kai don amfanin majalisae da kuma jihar ga baki daya.

KU KARANTA KUMA: Babu ruwana: Tinubu ya nisanta kansa daga masu masa kamfe din Shugaban kasa na 2023

Angibi, wanda ya samu wakilcin Salle Asiri, jigon APC a yankin, har ila yau yayi kira ga mabiya jam’iyyar da su cigaba da gudanar da addu’a da bada goyon baya ga sauran shuwagabanni don samun nasara.

Dan majalisan ya tabbatar ma mutanen mazabar shi cewa zai cika alkawarin da ya dauka don inganta rayuwar su.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel