Satar 'mitar wuta': Kotu ta daure wanzami, Nura Sulaiman

Satar 'mitar wuta': Kotu ta daure wanzami, Nura Sulaiman

Wata kotu mai daraja ta daya da ke zamanta a yankin Karu a Abuja ta yanke wa wani matashin wanzami, Nura Sulaiman, mai shekaru 21, hukuncin daurin watanni 15 a gidan yari bayan samunsa da laifin satar 'mitar wuta' guda biyar daga gidajen jama'a.

Mai laifin, mazaunin yankin Karu a Abuja, ya amsa laifukansa guda hudu da aka gurfanar da shi a kansu tare da neman afuwa da sassauci a hukuncin da za a yanke masa. An gurfanar da shi bisa tuhumarsa da aikata laifukan da suka hada da shiga wurin da bashi bda hurumi da aikata hakin bera.

Alkalin kotun, Sani Mohammed, ya bawa Sulaiman zabin biyan tarar N45,000.

Mohammed ya ce mai laifin bashi da wani uzuri na satar mitocin wutar tare da yi masa nasihar ya canja hali.

Tun da farko, mai gabatar da kara, Vincent Osuji, ya shaidawa kotun cewa wani mazaunin yankin Karu mai suna Abdulsalam Bolaji ne ya fara shigar da korafi a ofishin 'yan sanda na Karu a ranar 5 ga watan Yuli.

"Mai korafin ya sanar da jami'an 'yan sanda cewar an kama matashin wanzamin bayan ya haura gidansa a ranar 5 ga watan Yuli tare da sace masa mitar wutar.

“After he was arrested, four additional prepaid meters were found in the convict’s possession, which he confessed to have stolen from four different victims.

"Bayan an kama shi ne aka gano wasu mitocin hudu a tare da shi, wanda ya amsa da bakinsa cewa sato su ya yi," a cewar Osuji.

Laifukan matashin sun saba da sashe na 80, 348, 287, 319 da 306 na kundin 'Penal Code'.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel