Ku yi watsi da barazanar kungiyar arewa kan Ruga – Fadar Shugaban kasa ga yan Najeriya

Ku yi watsi da barazanar kungiyar arewa kan Ruga – Fadar Shugaban kasa ga yan Najeriya

Fadar shugaban kasa a ranar Talata, 9 ga watan Yuli, ta bayyana cewa ba a dakatar da shirin inganta lamarin dabbobi na kasa da Gwamnatin Tarayya ke son yi ba.

Yayin da take shawartan yan Najeriya kan cewa kada su damu da wa’adin kwana 30 da kungiyar arewa ta bayar akan shirin Ruga, fadar shugab kasa ta shawarci kungiyar da ta mutunta ofishin shugaban kasa wanda tace ta yake hukunci ne don ci gaban kasa.

Babban mai bada shawara kan harkokin gona a ofishin mataimakin shugaban kasa, Dr. Andrew Kwasari ya bayyana haka a wata hira tare da manema labarai a Abuja, a lokacin shirin horaswa da aka shirya don shugabannin kungiyar Miyyetti Allah da jami’anta a jihohi takwas a matsayin shirin wayar da kai.

Kakakin kungiyar arewa, Abdul-Azeez Suleiman, da suke bayar da wa’adin kwana 30 ga gwamnoni kan su amince da shirin Ruga, yace da wasu shugabannin yankin arewa ake hada baki don nakasa yankin.

Amman Kwasari yayi watsi da barazanar, inda yace mafi rinjaye na kasar sun mara wa Buhari baya akan dakatar da shirin Ruga.

KU KARANTA KUMA: Ya zama dole Buhari ya nada majalisarsa cikin gaggawa – Majalisar wakilai ta mika kokon bara a gaban Shugaban kasa

An tambaye shi ko zai bukaci a kama su, Kwasari yace ya tabbatar da cewa cibiyar tsaron kasar zata dauki mataki mai tsanani akan masu yin kalaman kiyayya da batanci.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel