Yanzu-yanzu: Wannan makon Buhari zai zabi ministoci - Shugaban majalisar dattawa

Yanzu-yanzu: Wannan makon Buhari zai zabi ministoci - Shugaban majalisar dattawa

Shugaba majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ya laburta a ranar Laraba cewa kafin wannan makon ya shude, shugaba Muhammadu Buhari zai aiko da jerin sunayen ministocin da yake nufin nadawa.

Ahmad Lawan ya bayyana hakan ne yayinda yake bada amsa kan jawabin da Sanata Albert Bassey Akpan na jam'iyyar PDP yayi inda yake nuna damuwarsa da jinkirin da fadar shugaban kasa keyi na aiko da jerin ministoci.

Akpan ya ce ta yaya shugaba Buhari ba zai aiko da sunayen ministoci ba, ana sauran makonni biyu yan majalisar si tafi dogon hutun watanni biyu da sukeyi.

Ya ce akwai bukatan fadar shugaban kasa ta hanzarta wajen aiko da sunayen saboda kada ya shafi hutunsu.

A cewar Sanata Lawan, fadar shugaban kasa na iyakan kokarinta wajen tabbatar da cewa majalisar dattawa ta samu takardan sunayen ministoci kafin makon nan ya shude.

Za ku tuna cewa a ranar Talata, kakakin majalisar dattawa, Dayo Adeyeye, ya ce ba hurumin majalisar bane fadawa Buhari lokacin da zai nada ministocinsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel