Rundunar yan sanda ta yi nasarar damke yan ta’adda masu yawa

Rundunar yan sanda ta yi nasarar damke yan ta’adda masu yawa

-Rundunar yan sanda ta jihar Nasarawa ta bayyana cewa ta kama masu aikata laifi guda 48 a fadin jihar.

-Komishinan yan sanda na jihar Nasarawa ne ya bayyana hakan inda ya kara da cewa sun kama wasu yan fashi guda biyu sun kuma kashe wani kasurgumin mai yin garkuwa da mutane

Rundunar yan sanda ta jihar Nasarawa ta bayyana cewa ta kama masu aikata laifi guda 48 a fadin jihar.

Komishinan yan sanda na jihar, Bola Longe ne ya bayyana haka a Lafiya inda ya ce “An kama duka masu laifin a wajaje daban daban bayan da muka tattara bayanan sirri.”

Ya bayyana cewa an kai masu rahoto a ofishinsu dake a Masaka a karamar hukumar Karu akan zargin hada kai wajen aikata laifi da kuma aikata laifin fashi da makami.

Komishinan ya bayyana cewa an kama mutum biyu a ranar 18 ga Yuni 2019 saboda suna da hannu a aikata laifin, inda kuma ya bayyana cewa an samu kananan bindigu biyu a hannunsu da kuma albarusai da kuma gatari.

KARANTA WANNAN: Babu ruwana: Tinubu ya nisanta kansa daga masu masa kamfe din Shugaban kasa na 2023

Komishinan ya kuma bayyana cewa an kama wani shi ma da zargin aikata fashi da makami, da yake amfani da gatari yana sarar mutane na yana kwace wayoyin su na hannu da kudade da wasu kayayyaki masu tsada. Ya bayyana cewa dan fashin na aikata laifin a kan hanyar Assakio da hanyar Ikposogye anan cikin jihar Nasarawa

Daga karshe kuma ya bayyana cewa an kashe wani kasurgumin dan garkuwa da mutane a wani musayar wuta da yan sanda sukayi da yan ta’addan a karamar hukumar Toto.

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel