Da duminsa: Bashin da ake bin Najeriya ya karu da N560bn a cikin wata uku

Da duminsa: Bashin da ake bin Najeriya ya karu da N560bn a cikin wata uku

- Yawan adadin kudin da ofishin kula da bashi ta saki a ranar Laraba, 10 ga watan Yuli ya nuna cewa bashin da ake bin kasar Najeriya ya karu

- Bashin dai ya karu ne da naira biliyan 560 cikin wata uku kacal

- DMP tace bashin ma’aji a ranar 31 ga watan Maris, 2019, ya kai naira triliyan 24.9 idan aka kwatanta da naira triliyan 24.3 da yake a ranar 31 ga watan Disamba 2018

Yawan adadin kudin da ofishin kula da bashi (DMO) ta saki a ranar Laraba, 10 ga watan Yuli ya nuna cewa bashin da ake bin kasar Najeriya ya karu da naira biliyan 560.

A cewar DMO, gaba daya adadin bashin ma’aji a ranar 31 ga watan Maris, 2019, ya kai naira triliyan 24.9 idan aka kwatanta da naira triliyan 24.3 da yake a ranar 31 ga watan Disamba 2018.

A wani labarin kuma, mun ji cewa Jihohi 12 da a ka samu canjin gwamnati a Najeriya su na dauke da bashin fiye da Naira tiriliyan 2 kamar yadda wani binciken da jaridar Daily Trust na Ranar 8 ga Watan Yulin 2019 ta yi, ya nuna.

Jaridar ta samu bayanan ta ne daga ofishin bashi na kasa na DMO, da hukumar da ke tara alkaluma a Najeriya, NBS da kuma sauran kwamitocin da gwamnoni ke nadawa domin karbar mulki.

KU KARANTA KUMA: Jami’in dan sanda ne ya harbi abokin aikinsa a lokacin zanga-zangarmu, ba mu bane – Yan shi’a

Jihohin da a ka bar wannan tarin bashi duk da irin kudin da su ke samu daga asusun FAAC na gwamnatin tarayya da bashin Paris Club su ne irin su Borno, Imo, Adamawa, Gombe, Oyo.

Sauran wadannan jihohi sun hada Yobe, Bauchi, Nasarawa, Ogun, Zamfara, Kwara da Legas. Face Yobe, Legas, Bauchi da Adamawa, wadannan gwamnoni duk sun yi shekaru 10 ne a kan mulki.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel