To fa: Osinbajo ya yi ma wani sanata habaici

To fa: Osinbajo ya yi ma wani sanata habaici

-Farfesa Yemi Osinbajo yace tsananin kaskanci ne marin mace

-Ba tare da kama suna ba, alamu sun tabbatar da cewa mataimakin shugaban kasa na yima sanata Elisha Abbo shagube ne

-Osinbajo ya bada labarin wani lamari da ya afku, inda wani mutum ya mari wata yar talla da kuma yadda aka kusan rufe maganar

Mataimakin shugaban kasar Najeriya, Yemi Osinbajo ya ce kaskanci ne da wulakanci marin mace. Osinbajo ya bayyana haka ne a wajen taron kaddamar da takardar tarihi da tsohon gwamnan jihar Ogun, Olusegun Osoba ya rubuta.

Mataimakin shugaban kasan ya bada labarin wani lamari da ya afku tun tuni inda wani dan Najeriya da aka haifa a kasar Birtaniya, Patrick Chadwick ya mari wata yar talla mai suna Adekunbi Adeite, a shagon Kingsway da ke a jihar Legas.

Osinbajo yayi Allah wadai da dabi’ar marin mata inda ya kwatanta dab’iar a matsayin “harkar kaskanci.”

KARANTA WANNAN: Allah ya kyauta: Dalibi dan shekara 14 ya bayyana dalilin da ya sanya ya shiga kungiyar asiri

Ba tare da kama suna ba, alamu sun nuna cewa Osinbajo na yima sanata Elisha Abbo habaici ne, wanda kwanan nan ya mari wata mace mai shayarwa a shagon kayan wasan jima'i da ke a Abuja.

Mataimakin shugaban kasan ya bayyana cewa a lokacin da Osoba yake dan jarida, ya fallasa aika aikar Patrick Chadwick, wanda hakan ya sanya Patrick dole ya ajiye aikinsa kuma aka hukuntashi.

Bayan da ya gama bada labarin irin gwagwarmayar da Osoba yayi a matsayinshi na dan jarida tun lokacin yakin basasa, Osinbajo bayyana cewa Osoba ne dan jaridan yayi binciken kwakwab ya gano yadda Patrick ya mari Adekunbi a jihar Legas.

Osinbajo ya bayyana cewa dalilin wannan fallasa ya sanya maganar ta zama “Maganar da ake zantawa a duk fadin kasa wanda hakan ya sanya UAC ta hukunta mai laifin kuma ya ajiye aikinshi.”

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel