Babu ruwana: Tinubu ya nisanta kansa daga masu masa kamfe din Shugaban kasa na 2023

Babu ruwana: Tinubu ya nisanta kansa daga masu masa kamfe din Shugaban kasa na 2023

- Bola Tinubu ya nisanta kansa daga wasu kayayyakin yakin neman zaben shugaban kasa na 2023 da ke yawo

- Babban jigon APC na kasa ya bayyana yin amfani da yada kayan yakin neman zabe a matsayin “mara cancanta kuma wanda ba a bukata”

- A cewar Tinubu, bai da masaniya akan kungiyar ko kayayyakin da take rarrabawa

Jigon jam’iyya mai mulki na kasa ya nisanta kansa daga lamarin kayayyakin yakin neman zabe a 2023 wanda aka yada a titunan Legas da sauransu.

Tinubu yace kayan wanda kungiyar da ke taya shi yakin neman zabe take rabawa akan ra’ayinsa na shugabancin kasa a 2023 bai cancanta ba.

Kakakin babban jigon APC na kasa, Tunde Rahman a wani jawabin da yayi ya bayyana kayan a maysayin kayan a matsayin wanda ake rarrabawa ba tare da izinin Tinubu ba.

KU KARANTA KUMA: Majalisar dattawa ga fadar Shugaban kasa: Muna jiran sunayen ministoci

Ya jadadda cewa Tiubu bai da masaniya akan kungiyar ko kayayyakin da take rarrabawa.

A wani labari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa Jam’iyyar adawa ta PDP ta fara gabatar da shaidunta a gaban kotun da ke sauraron karar zaben 2019 a shari’ar da ta ke yi da APC ‘dan takarar ta watau shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Daga cikin wadanda su ka fara bada shaida akwai Injiniya Buba Galadima, wanda a da can ya na cikin ‘yan gani-kashe-ni na shugaba Muhammadu Buhari a lokacin a na jam’iyyar hamayya.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel