Ya zama dole Buhari ya nada majalisarsa cikin gaggawa – Majalisar wakilai ta mika kokon bara a gaban Shugaban kasa

Ya zama dole Buhari ya nada majalisarsa cikin gaggawa – Majalisar wakilai ta mika kokon bara a gaban Shugaban kasa

- Majalisar wakilai na so Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada mambobin majalisarsa cikin gaggawa

- Hon Toby Okechukwu ne ya gabatar da bukatar a gaban majalisar wakilai

- Sai dai kuma Hon Mohammed Monguno, yayi adawa da korafin ta hanyar tunatarwa, cewa kundin tsarin mulki ta samar da iya lokacin da Shugaban kasar zai ada ministoci ba

Majalisar wakilai a ranar Talata, 9 ga watan Yuli, ta bukaci shugban kasa Muhammadu Buhari da yayi gaggawan nada majalisar da za su yi aiki tare da shi a shekaru hudu masu zuwa.

Channels Television ta ruwaito cewa Hon Toby Okechukwu ne ya gabatar da bukatar a gaban majalisar wakilai lokacin zaman majalisar.

Kafin majalisar ta yanke hukunci, sai wani dan majalisa, Hon Mohammed Monguno, yayi adawa da korafin ta hanyar tunatarwa.

Monguno yayi korafin cewa kundin tsarin mulki ta samar da iya lokacin da Shugaban kasar zai ada ministoci ba.

KU KARANTA KUMA: Jami’in dan sanda ne ya harbi abokin aikinsa a lokacin zanga-zangarmu, ba mu bane – Yan shi’a

Sai dai kuma Okechukwu, ya bayyana cewa a cikin korafin da ya gabatar bai ce akwai wani lokaci na nadin ministocin ba.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Majalisar dattawan Najeriya a ranar Talata, 9 ga watan Yuli tace a shirye take ta karbi jerin sunayen ministoci daga fadar Shugaban kasa a duk lokacin da ta gabatar da shi.

Sai dai kuma, Majalisar dattawan tace jinkiri wajen gabatar da sunayen ministocin daga Shugaban kasa Muhammadu Buhari ba zai hana sanatoci tafiya hutunsu na shekara da suka shirya ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel