Alkaluma sun nuna Atiku Abubakar ne ya lashe zaben 2019 Inji Buba Galadima

Alkaluma sun nuna Atiku Abubakar ne ya lashe zaben 2019 Inji Buba Galadima

Jam’iyyar adawa ta PDP ta fara gabatar da shaidunta a gaban kotun da ke sauraron karar zaben 2019 a shari’ar da ta ke yi da APC ‘dan takarar ta watau shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Daga cikin wadanda su ka fara bada shaida akwai Injiniya Buba Galadima, wanda a da can ya na cikin ‘yan gani-kashe-ni na shugaba Muhammadu Buhari a lokacin a na jam’iyyar hamayya.

A wata zantawa da BBC Hausa, Buba Galadima ya bayyana dalilin bayyanarsa a gaban kotu ya na nema a karbe nasarar da APC ta samu a zaben bana. Galadima ya nun ya na da dalilai har biyu.

Injiniya Buba Galadima ya bayyana cewa babban abin da ya shaidawa kotu shi ne shugaba Buhari bai da cikakken ilmin da zai jagoranci ragamar Najeriya kamar yadda dokar kasar nan ta tanada.

KU KARANTA: An tambayi Lauyoyi game da iya Ingilishin Shugaba Buhari

Galadima ya ce Atiku ne wanda ya ke da ilmi da sanin tattalin arziki, kuma ‘dan takarar da zai iya kawo zaman lafiya a Najeriya, a cewarsa wannan ya sa Kungiyarsa ta r-APC ta mara masa baya.

Bayan haka kuma tsohon jigon na APC ya tabbatar da cewa alkaluman da su ke da shi, ya nuna cewa ‘dan takarar PDP, Alhaji Atiku Abubakar shi ne ya lashe zaben shugaban kasa da a ka yi.

Buba Galadima, wanda ya taba zama Sakataren jam’iyyar CPC mai adawa, ya fadawa Manema labarai cewa sun gabatar da takardu a gaban kotu da ke gaskata cewa PDP ce ta lashe zaben 2019.

Babban ‘dan siyasar ya dai nuna cewa har yanzu ya na cikin jam’iyyar APC mai mulki, kuma babu wanda ya isa ya koresa daga wannan jam’iyya da a kafa da guminsu a shekarun baya can.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel