Duk dan sandan da ya karba kudin beli bashi da banbanci da mai garkuwa da mutane - Kwamishinan 'Yan sanda

Duk dan sandan da ya karba kudin beli bashi da banbanci da mai garkuwa da mutane - Kwamishinan 'Yan sanda

Kwamishinan 'Yan sanda na jihar Legas, Zubairu Mu'azu ya ce 'yan sandan da ke karbar kudin baili sun fi masu garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa muni.

Shugaban na 'Yan sanda ya yi fadi hakan ne a ranar Talata a garin Legas yayin da ya ke jawabi wurn taron kaddamar da dakin rubuta shaida a Sashin Binciken Masu Aikata Manyan Laifuka (SCIID) a Panti.

Shugaban na 'yan sanda ya kuma ja kunnen jami'ansa da su guji karbar cin hanci daga hannun mutanen da suka kama saboda hakan yana bata wa rundunar suna a idon duniya.

DUBA WANNAN: Jerin sunaye: Mutum 5 da suka mallaki arzikin da ya fi kasafin kudin Najeriya

"Ina bamu shawara mu guji karbar rashawa. Hakan na ba ta mana suna saboda hakan ya sabawa dokar aiki da tarbiya.

"Kamar yadda muka sha fadi, ba a karbar kudi kafin bayar da beli. Na sha fada cewa duk dan sandan da ya karba kudin beli bashi da banbanci da mai garkuda da mutane. Banbancin kawai shine kowa ya san inda ka ke rike da wanda kayi garkuwa da su.

"Muna cikin mawuyacin hali a Najeriya kuma muna bukatar mutane fiye da yadda muke bukatarsu. Ya kamata mu nesanci cin hanci da rashawa," inji Zubairu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel