Jami’in dan sanda ne ya harbi abokin aikinsa a lokacin zanga-zangarmu, ba mu bane – Yan shi’a

Jami’in dan sanda ne ya harbi abokin aikinsa a lokacin zanga-zangarmu, ba mu bane – Yan shi’a

- Kungiyar shi'a tayi ikirarin cewa rundunan yan sandan Najeriya tayi hayan yan tasha don hargitsa zanga zangar da kungiyar tayi a ranar Talata

- Ta yi zargin cewa jami'in dan sanda ne ya harbi abokin aikin shi amma ba su ba kamar yadda ake ikirari

- Yan shi'an sun jadadda cewar za su ci gaba da zanga-zanga har sai an saki shugabansu

Kungiyar mabiya addinin Shi’a na Najeriya tayi ikirarin cewa rundunan yan sandan Najeriya tayi hayan yan tasha don hargitsa zanga zangar da kungiyar tayi a ranar Talata, 9 ga watan Yuli.

An kashe yan shi’a biyu sannan yan sanda hudu sun ji rauni, yayinda aka fasa motoci 50 sanadiyar rikicin da ta barke a lokacin gudanar da zanga zangar.

Yan sandan a baya sunyi ikirarin cewa masu zanga zangar sunyi yunkurin shiga zauren majalisar tarayya da ke harabar Majalisar dokoki ta hanyar haura katanga.

An kama yan shi’a guda 40 a lokacin hatsaniyan.

Abdullahi Musa, kakakin kungiyar shi’a ya bayyana cewa yan sanda sunyi hayan yan tasha don su saje da masu zanga zangar.

Har ila yau ya bayyana cewa daya daga cikin yan sandan da yayi harbi kan yan zanga zangar ne ya harbi abokin aikinsa cikin kuskure.

KU KARANTA KUMA: Tsugunne ba ta kare ba: Ku shirya muna nan dawowa gare ku - 'Yan Shi'a sun gargadi jami'an tsaro

Musa a baya ya fada ma SaharaReporters cewa “zanga zangan zai cigaba da gudana akan bukatar a saki shugabanmu, kungiyan zata gidanar da gagarumar zanga zanga a yau Laraba.

“Har ila yau kashe mambobinmu biyu da yan sanda suka kashe ba zai hana ayi zanga zangar ba.”

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel