Gwamnatin Tarayya ta fara kidayar dabbobi da yi masu shaida a Najeriya

Gwamnatin Tarayya ta fara kidayar dabbobi da yi masu shaida a Najeriya

- Gwamnatin Najeriya ta fara kidaya, tantancewa da yiwa dabbobi shaida a kasar nan

- Gwamnatin ta ce hakan zai taimaka wajen magance annobar satar shanu tare da sanin ainihin adadin dabbobin kiwo dake kasar nan

- Gwamnatin ta kuma ce saura kiris ta kammala shimfidar dokoki na samar wa da mallakar shanun kiwo

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta fara gudanar da kidaya, tantancewa, tare da lamɓatawa dabbobin kiwon shaida a fadin kasar nan.

Babban sakataren dindindin na ma'aikatar noma da raya karkara ta kasa, Dakta Muhammad Bello Umar, shi ne ya bayar da shaidar hakan cikin wata sanarwa a karshen makon da ya gabata a garin Abuja.

A cewar sa, wannan yunkurin zai taimaka kwarai da aniya tare da taka muhimmiyar rawar gani wajen magance mummunar ta'adar satar shanu tare da samun masaniyar ainihin adadin dabbobin kiwo dake kasar nan.

Jagoran cibiyar kula da lafiyar dabbobi kiwo, Bright Wategire, shi ne ya wakilci babban sakataren yayin taron karawa juna sani da aka gudanar dangane da muhimmancin kidayar dabbobi da kuma tantancewa.

KARANTA KUMA: Majalisar Dattawa ta nemi a shimfida dokar hukuncin kisa kan masu aikata laifin fyade

Bright ya ce a halin yanzu saura kiris gwamnatin Tarayya ta kammala shirye-shiryen ta na shimfida dokoki na samar wa da kuma mallakar shanu na kiwo.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel