Tsugunne ba ta kare ba: Ku shirya muna nan dawowa gare ku - 'Yan Shi'a sun gargadi jami'an tsaro

Tsugunne ba ta kare ba: Ku shirya muna nan dawowa gare ku - 'Yan Shi'a sun gargadi jami'an tsaro

- Muna nan fito yau, gargadin 'yan kungiyar 'yan uwa Musulmai kenan ga hukumar 'yan sanda

- Sun ce abu daya ne zai hana su fitowa, shine idan an saki shugaban su, an kuma barshi ya tafi neman magani

- Jiya ne dai 'yan shi'an suka kai wa wasu jami'an 'yan sanda da suke gadin kofar majalisar tarayya a Auja, inda suka harbi wasu daga cikinsu kuma suka kone motoci

'Yan kungiyar 'yan uwa Musulmai, wadanda aka fi sani da 'yan shi'a, sun sha alwashin sake fitowa yau Laraba domin sake gabatar da wata zanga-zangar a Abuja, duk da dauki ba dadin da suka yi da jami'an hukumar 'yan sanda da ke gadin majalisar tarayya jiya Talata a Abuja.

Jaridar Sahara Reporters ta gano cewa 'yan shi'ar zasu sake fitowa da sabon tsari, inda suka sake hada karfi da karfe domin sake gabatar da wata gagarumar zanga-zangar yau Larabar nan a Abuja.

A zanga-zangar da suka yi jiya a Abuja, an kashe 'yan Shi'a biyu, yayin da aka yiwa 'yan sanda guda biyar rauni, aka kuma kone motoci guda 50.

KU KARANTA: Wani matashi ya kashe kanshi bayan abokin aikinsa ya zabga masa karyar cewa an koreshi a aiki

Sakataren kungiyar 'yan shi'ar, Abdullahi Musa ya bayyanawa Sahara Reporters cewa kashe mutane biyun da aka yi musu ba zai saka su tsorata ba.

"Muna nan fitowa yau Laraba. Abinda kawai zai hana mu fitowa shine idan an saki shugaban mu kuma, an barshi ya tafi neman magani," in ji Musa.

'Yan shi'ar suna ta gabatar da zanga-zanga a cikin birnin tarayyar sama da makonni uku da suka, inda suka bukaci gwamnati ta saki shugaban nasu, wanda aka kama tun shekarar 2015, duk kuwa da cewa kotu ta bayar da umarnin a sake shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel