Wani matashi ya kashe kanshi bayan abokin aikinsa ya zabga masa karyar cewa an koreshi a aiki

Wani matashi ya kashe kanshi bayan abokin aikinsa ya zabga masa karyar cewa an koreshi a aiki

- Wani matashi ya kashe kansa a cikin karshen satin nan da ya gabata saboda an kore shi a aiki

- Hakan ya biyo bayan labarin karya da wani abokin aikinsa ya kawo masa na cewa an koreshi daga gurin aikinsu

- Bayan haka kuma saboda wannan labari ne budurwarsa wacce suka shafe shekara uku suna tare ta gudu ta koma gurin abokinsa

Wani mutumi mai amfani da shafin Twitter ya wallafa wani labari a shafinsa, inda yake cewa, akwai wani labari da ya kamata ya sanar da mutane akan abinda ya faru da abokinsa Deji, wanda ya sani da dadewa, sai gashi ya kashe kanshi jiya.

Abokin aikinsa ne ya kawo mishi labarin karya na cewa an kore shi daga aiki, sannan kuma budurwarsa wacce suka shafe shekaru uku suna tare ta gudu ta koma wurin abokinsa, saboda wannan dalilin.

KU KARANTA: Allah Sarki: Ina jin bani da rabon hawa kujerar gwamnar jihar Taraba - Mama Taraba

Bayan mutuwarsa gaskiya ta fito a gurin aikin nasu, yayin da shugabansu yayi masa karin mukami, ya bashi sabuwar mota. Kawai sai yake samun labarin cewa ya kashe kanshi.

Rahotanni sun nuna cewa shugaban nasu ya saka a kama abokin da ya yayi karyar cewa an kori Deji daga aikin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel