Majalisar dattawa ga fadar Shugaban kasa: Muna jiran sunayen ministoci

Majalisar dattawa ga fadar Shugaban kasa: Muna jiran sunayen ministoci

- Majalisar dattawa tace a shirye take ta karbi jerin sunayen ministoci daga fadar Shugaban kasa a kowani lokaci

- Majalisar dattawar ta bayyana cewa jinkiri wajen gabatar da sunayen ba zai hana sanatoci tafiya hutunsu na shekara da suka shirya ba

- Yan majalisar tarayyar na shirin fara hutunsu na shekara a karshen Yuli, 2019

Majalisar dattawan Najeriya a ranar Talata, 9 ga watan Yuli tace a shirye take ta karbi jerin sunayen ministoci daga fadar Shugaban kasa a duk lokacin da ta gabatar da shi.

Sai dai kuma, Majalisar dattawan tace jinkiri wajen gabatar da sunayen ministocin daga Shugaban kasa Muhammadu Buhari ba zai hana sanatoci tafiya hutunsu na shekara da suka shirya ba.

Yan majalisar tarayyar na shirin fara hutunsu na shekara a karshen Yuli, 2019, jaridar Thee Nation ta ruwaito.

Shugaban kwamitin majalisar dattawa kan harkokin labarai da jama’a, Sanata Adedayo Adeyeye, wanda yayi jawabi ga manema labarai a Abuja yace ba hakki majalisar dattawa bane kayyade lokacin gabatar da sunayen ministoci.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya aika ma majalisa sunayen mutane 5 da zai nada muhimman mukamai

Adeeyeye ya kuma bayyana cewa kundin tsarin mulki bai ba majalisar dattawa ikon tambayan sunayen daga fadar Shugaban kasa ba.

Majalisar dattawan, yace za ta ci gaba da jira har zai Shugaban kasar ya yanke hukuncin tura mata sunayen.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel