Majalisar Dattawa ta nemi a shimfida dokar hukuncin kisa kan masu aikata laifin fyade

Majalisar Dattawa ta nemi a shimfida dokar hukuncin kisa kan masu aikata laifin fyade

Damuwa da yadda mummunar ta'adar cin zarafi da keta haddi musamman na zakkewa mata masu kananun shekaru a fadin kasar nan, majalisar dattawa ta nemi a shimfida dokar hukuncin kisa kan miyagun da ke aikata wannan alfasha.

Majalisar dattawan Najeriya ta kuma umurci kwamitocin ta a kan harkokin shari'a, 'yan sanda, harkokin mata, da kuma ci gaban zamantakewa, da su gaggauta kulla dangartaka tare da dukkanin masu ruwa da tsaki domin kare martabar mata a kasar nan musamman masu kananan shekaru.

Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, majalisar dattawan Najeriya na neman a malala tsare-tsare da dokokin cikin kundin tsarin mulkin kasar nan domin tabbatar da kariya ga martaba da kuma tsare mutuncin mata masu kananan shekaru daga afkawa cikin zaluncin fyade da keta haddi.

Majalisar ta kuma nemi kwamitocin ta maus ruwa da tsaki da su gudanar da nazari mai zurfin gaske waje shifida dokoki da tsauraran matakai na hukunta dukkanin masu cin zarafin mata ta hanyar fyade da keta haddi musamman da a wani sa'ilin take aukuwa a kan jarirai.

Ta nemi a tilastawa hukumar 'yan sanda da sauran hukumomin tsaro a kan horar da jami'ai masu yaki laifukan fyade da sauran dangin laifuka masu nasaba da keta haddin mata masu kananan shekaru.

KARANTA KUMA: Dalilin da ya sa nake son zama gwamnan jihar Kogi - Dino Melaye

Majalisar ta tattauna batutuwa a kan wannan mummunar annoba dake neman zama ruwan dare a kasar nan bisa ga shawarar wakiliyar shiyyar Cross River ta Arewa a majalisar dattawa, Sanata Rose Oko ta jam'iyyar PDP.

Sanata Rose ta yi babatu tare da bayyana takaicin yadda ake cin zarafin Mata 6 cikin kowane 10 a kowace rana cikin kasar nan, yayin da ta hikaito labarin yadda aka zakkewa wata jaririya 'yar watanni shida a jihar Kano da kuma yadda ta'adar fyade ta yadu a tsakanin malamai da kuma daliban su.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel