Zan yi yaki da rashin gaskiya kamar yadda mu ka yi alkawari a Gombe – Inji Gwamna Yahaya

Zan yi yaki da rashin gaskiya kamar yadda mu ka yi alkawari a Gombe – Inji Gwamna Yahaya

Mai girma gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya, ya bayyana cewa zai yi yaki da masu satar dukiyar gwamnati tare da tabbatar da gaskiya a gwamnatinsa. Gwamnan ya bayyana wanan ne a jiya.

Inuwa Yahaya ya kai wa Sakataren gwamnatin tarayyar Najeriya watau Boss Mustapha ziyara a baban birnin tarayya Abuja. Yahaya ya ziyarci SGF din ne jim kadan bayan ya koma kan mukaminsa.

Gwamnan ya kai wa Boss Mustapha wannan ziyara ne domin karfafa dagantakar da ke tsakanin jiharsa da gwamnatin tarayya. Yahaya ya ce Gombe za ta cigaba da tafiya da tsaren-tsaren shugaba Buhari.

KU KARANTA: Buhari ya yi wasu sababbin nade-nade a hukumar NCC

Kamar yadda rahoto zo mana, Gwamnan na Gombe ya nuna cewa ya na bin sahun gwamnatin Buhari na yaki da rashin gaskiya. Gwamnan ya bayyana wannan ne ta bakin Hadiminsa, Ismaila Misilli.

A jawabin da mai ba gwamnan shawara kan harkokin yada labarai ya fitar, Ismaila Uba Misilli, ya ce gwamnatin Gombe ta na nan a kan muradun jam’iyyar APC da manufofin gwamnatin shugaba Buhari.

Gwamnan ya ce:

“A matsayinmu na gwamnati, mun san da hakkin jama’a da nauyin mutane da ke kanmu, kuma za mu yi kokari wajen kawo canjin da al’umma su ke muradi kamar yadda mu ka yi wa mutanen Gombe alkawari.”

A jawabin gwamnan ya yi amfani da wannan dama wajen taya Boss Mustapha murnar sake nada shi da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi a matsayin Sakataren gwamnatin tarayyar kasar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel