Gobara ta lashe kasuwar kantin Amigo da ke Abuja

Gobara ta lashe kasuwar kantin Amigo da ke Abuja

-Gobara ta lashe babbar kasuwar kanti da aka fi sani da 'Amigos supermarkets' da ke a Wuse 2 Abuja

-Gobarar ta shafi bangaren ajiye kaya ne na kasuwar kuma ta tashi da misalin karfe 1:30 na rana a jiya Talata 9 ga watan Yuli 2019-07-10

-Rundunar yan sanda ta bayyana cewa yan kwana kwana sun yi nasarar kashe gobarar da misalin karfe 7:30 na yamma

A jiya Talata 9 ga watan Yuli 2019, gobara ta tashi a wannan babbar kasuwar kanti da mutane ke so wadda aka fi sani da Amigos supermarket.

Jami’in hulda ta jama’a na rundunar yan sanda ta babban birnin tarayya, Jerry Timvh ya tabbatar da afkuwar lamarin ga kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN).

Timvh ya bayyana cewa gobarar ta tashi ne da misalin karfe 1:30 na rana kuma ta shafi bangaren ajiya ne kawai na kantunan, inda kuma ya bayyana cewa yan kwana kwana sun yi nasarar kashe gobarar da misalin karfe 7:30 na yamma.

Timvh ya bayyana cewa har yanzu ba a gano sanadin gobarar ba amma ya ce rundunar su na nana na bincike don gano musabbabin tashin gobarar.

KARANTA WANNAN: Yan bindiga sun yi barna yayin da suka kai farmaki gidan marayu

Timvh ya bayyana cewa “Gobarar tayi sanadiyyar rasa kayayyaki masu yawa dake a dakin ajiyar amma ba a san takamaimai asarar nawa akayi ba.”

Ya kara da cewa “Gobarar ba ta shafi cikin kantunan ba saboda anyi kokarin tsayar da wutar ta yadda ba za ta yadu sosai ba.”

“Ba a samu asarar rai ko daya ba, saboda masu kantunan da sauran masu aiki sun samu sun fita daga cikin shagunan tun kafin wutar ta fara ci.” A cewarshi.

An canza ma 'Amigos supermarket' suna zuwa '4U supermarket' a shekarar 2015.

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel