Tirkashi: Ba ku isa ku dakatar dani ba, saboda nima Sanata ne tamkar ku - Sanata Abbo ya gargadi Sanatoci

Tirkashi: Ba ku isa ku dakatar dani ba, saboda nima Sanata ne tamkar ku - Sanata Abbo ya gargadi Sanatoci

- Sanata Elisha Abbo, wanda aka kama dumu-dumu a kyamara yana marin wata mata, ya bayyana a gaban kwamitin Sanatoci, wacce aka shirya domin ta bincike shi akan lamarin, jiya Talata 9 ga watan Yuli

- An ruwaito cewa Sanata Abbo yaki yin magana a gaban manema labarai da kwamitin Sanatocin, abinda ya jawo cece-kuce kenan da Sanata Oluremi Tinubu

- Abbo ya gayawa matar Tinubu cewa ta daina tsorata shi da cewar za a dakatar dashi saboda shi ma Sanata ne tamkar ta

Sanata Elisha Abbo, wanda aka kama dumu-dumu a kyamara yana marin wata mata, ya bayyana a gaban kwamitin Sanatoci, wacce aka shirya domin ta bincike shi akan lamarin, jiya Talata 9 ga watan Yuli.

A yadda jaridar Premium Times ta ruwaito ta bayyana cewa, Sanatan na jihar Adamawa, ya ki yarda yayi magana a gaban manema labarai da kuma kwamitin Sanatocin.

Legit ta gano cewa kafin a bari mutum ya fara magana, sai ya fara yin rantsuwa a gaban kwamitin, wacce za ta nuna cewa gaskiya mutum zai fada.

Sai dai kuma shi Abbo ya bukaci a barshi ya fara yin magana kafin ya rantse, abinda ya kawo kace-nace kenan tsakaninsa da 'yan kwamitin.

Daya daga cikin 'yan kwamitin, Sanata Oluremi Tinubu, ta bukaci Abbo ya fara rantsewa kafin yace komai. Amma yaki yarda, inda ya ce komai na hannun kotu.

KU KARANTA: To fah: An nemi a hallaka saurayin nan da ya angwance ta shafin Facebook a Kano

Ya ce: "Wannan lamarin yana kotu. Babu yadda za ayi a dinga daukana a kyamara bayan komai yana hannun kotu."

Tinubu ta mai da masa da martani kamar haka: "Baka jima da shigowa wannan majalisar ba. Muna da hanyoyi na yadda muke gabatar da lamuran mu, kuma mu ma muna karkashin doka ne. Ba zai yiwu ka shigo nan ka gaya mana yadda zamu yi abu ba.

"Kai ne mai laifi yanzu. Ba ka isa ka gaya mana abinda zamu yi ba, saboda zamu iya dakatar da kai."

Bayan maganar Tinubu, cikin fushi Abbo ya ce: "Ba zan iya zama a nan ba kuna yi mini barazanar dakatar dani ba. Ni ma Sanata ne tamkar ku."

An danyi rikicin na tsawon wasu mintuna, daga baya kuma aka bukaci manema labarai da su bar wurin domin cigaba da ganawa dashi cikin sirri.

Idan ba a manta ba ranar Litinin dinnan ne, jami'an 'yan sanda suka gurfanar da Sanata Elisha Abbo a kotun majistire dake Zuba, Abuja, da laifin cin Zarafin wata mata mai ciki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel