Kwamitin Buhari ya bankado Biliyan 3 a hannun Jami’an hukumar PEF

Kwamitin Buhari ya bankado Biliyan 3 a hannun Jami’an hukumar PEF

Kwamitin nan na SPIP da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada domin bincike da kuma karbe kadarorin gwamnatin Najeriya da ke hannun ma’aikata ya yi wani babban kamu kwanan nan.

Kamar yadda mu ka samu labari daga Daily Trust a yau Ranar 10 ga Watan Yuli, 2019, kwamitin na SPIP ya gano fiye da Naira biliyan uku a cikin asusun bankin wasu ma’aikatan gwamnatin tarayya.

Shugaban wannan kwamiti watau Okoi Obono-Obla, ya bayyanawa Duniya cewa sun bankado wannan kudi ne daga cikin asusun Dr Goody Nnadi da and Aisha F. Usman da ke aiki da hukumar nan ta PEF.

Okoi Obono-Obla ya bayyana wannan ne lokacin da ya tara Manema labarai a Abuja, inda ya sanar da Duniya cewa kwamitinsa sun gano wannan kudi ne bayan korafi da a ka kai masu kwanakin baya.

KU KARANTA: Kotun koli ta yi fatali da karar da a ka kai wani ‘Dan Majalisa a 2019

Mista Goody Nnadi ya bude akawun ne da sunan wani kamfanin otel mai suna Galbani and Greatwood Hotels a Garin Owerri ta jihar Imo. An samu Naira biliyan 2.2 a cikin wannan akawun da kuma Daloli.

Haka zalika Aisha Usman Manaja ce kamar Nnadi a wannan hukuma ta PEF mai kula da harkar mai a Najeriya. An gano wani akawun guda mai dauke da fiye da Naira biliyan 1.4 a ciki da sunan wannan Baiwar Allah.

A asusun na Nnadi mai dauke da sama da Biliyan 2, an samu Dala $302,964, fam €11,000 da kuma fam £2,000 na kudin kasar Ingila. A na zargin duk wannan cin hanci ne da wasu su ka rika ba ma’aikatan.

Bayan wannan kuma akwai wasu takardun mallakar kadarori da a ka samu a hannun manyan jami’an gwamnatin, ban da kuma kudin kasar waje na Dala 100, fam €200. Obla ya ce za su shigar da kara a kotu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel