Yan bindiga sun yi barna yayin da suka kai farmaki gidan marayu

Yan bindiga sun yi barna yayin da suka kai farmaki gidan marayu

Wasu gungun yan bindiga sun afka wani gidan da ake kulawa da marayu da gajiyayyu, Great Saints Orphanage dake garin Issele-Uku cikin karamar hukumar Aniocha ta Arewa na jahar Delta.

Rahoton jaridar New Nigerian ta bayyana cewa yan bindigan sun lalata wani sashi na gidan tare da barnata wasu motoci dake ajiye a farfajiyar gidan marayun, kamar yadda mai gidan, Emeka Ezeagbor ya bayyana.

KU KARANTA: Buhari ya aika ma majalisa sunayen mutane 5 da zai nada muhimman mukamai

Mista Emeka ya bayyana damuwarsa da harin, inda yace bai san dalilin da zai sa wani mutumi dauke da makami zai kai hari gidan marayu da gajiyayyu, har su lalatashi ba. Shima shugaban kungiyar jama’an Issele ya bayyana cewa zasu dauki mataki akan lamarin.

Shugaban jama’an, Ugeh Ofordile ya bayyana cewa sun fara gudanar da zaman tattaunawa a tsakanin al’ummar yankin domin gano musabbabin kai harin da yan bindigan suka kai, tare da daukan matakin daya dace don magance hakan a gaba.

A wani labara kuma, wani mutumi mai suna Joshua Alexander Shehu ya kashe diyarsa yar shekara 11 a karamar hukumar Akwangan jahar Nassarawa bisa zarginta da yake yi da shiga kungiyar matsafa tare da aikata miyagun ayyukan tsafe tsafe.

Wannan lamari ya faru ne a ranar Lahadin data gabata, inda Joshua ya halaka karamar yarinyarsa mai suna Jessican a kan zarginta da yake yin a kashe mahaifiyarsa a shekarar 2017.

Haka zalika Joshua yana zargin Jessica da daura ma amaryarsa daya aura cututtuka da rashin lafiya, bayan ya saki mahaifiyarta, don haka ya tabbatar ma kansa cewa mayyace, kuma ya yanke shawarar kasheta kafin ta kashe masa mata kamar yadda ta yi ma uwarsa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel