Ke duniya: Ya kashe diyarsa a kan zarginta da kashe mahaifiyarsa ta hanyar tsafe tsafe

Ke duniya: Ya kashe diyarsa a kan zarginta da kashe mahaifiyarsa ta hanyar tsafe tsafe

Wani mutumi mai suna Joshua Alexander Shehu ya kashe diyarsa yar shekara 11 a karamar hukumar Akwangan jahar Nassarawa bisa zarginta da yake yi da shiga kungiyar matsafa tare da aikata miyagun ayyukan tsafe tsafe.

Rahoton jaridar NewNigerian ta ruwaito wannan lamari ya faru ne a ranar Lahadin data gabata, inda Joshua ya halaka karamar yarinyarsa mai suna Jessican a kan zarginta da yake yin a kashe mahaifiyarsa a shekarar 2017.

KU KARANTA: Kotu ta daure wata budurwa shekara 11 a Kurkuku saboda cin mutuncin Ganduje

Haka zalika Joshua yana zargin Jessica da daura ma amaryarsa daya aura cututtuka da rashin lafiya, bayan ya saki mahaifiyarta, don haka ya tabbatar ma kansa cewa mayyace, kuma ya yanke shawarar kasheta kafin ta kashe masa mata kamar yadda ta yi ma uwarsa.

Tuni jami’an Yansanda suka cika hannu da Joshua, inda suka mikashi zuwa babban ofishin binciken manyan laifuka rundunar Yansanda, watau CID, dake garin Lafiya don cigaba da gudanar da bincike.

A wani labarin kuma, wani saurayi mai suna Emmanuel Sunday ya hada baki budurwarsa, Chinaza Nwogu suka yi garkuwa da mahaifinta mai shekaru 88 a duniya, Pa Njoku-Louis, wai don su samu kudin fansa da zasu gudanar da bikin aurensu dashi.

Kaakakin rundunar Yansandan Najeriya, DCP Frank Mba ne ya bayyana haka yayin da yake bayyana mutanen ga manema labaru, inda yace Sunday dan shekara 29 ya hada baki da Chinaza yar shekara 19 da kuma dan uwanta wajen sace surukinsa.

Kaakakin yace manufar mutanen uku na yin garkuwa da wannan tsoho shine domin iyalansa su biyasu kudin fansa, ta yadda zasu samu isashshen kudi da zasu gudanar da bikin aurensu dasu sakamakon Chinaza tana dauke da ciki wata 8, ka ga sai a sha shagali iya shagali.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel