Bamu san ranar da lantarki za ta tsaya ba a Najeriya – DISCO

Bamu san ranar da lantarki za ta tsaya ba a Najeriya – DISCO

-Kamfanin bayar da wutar lantarki na Abuja ya ce babu ranar samun tsayayyar wutar lantarki a Najeriya

-Babban daraktan kamfanin shi ne yayi wannan furuci yayin da yake gabatar da jawabinsa wurin wani taro a Minna ta jihar Neja

-A cewar darakta babban matsalar da kamfanin nasu ke fuskanta a halin yanzu ita ce amfani da tsoffin kayan aiki da ya kamata a ce a canzasu

Kamfanin bayar da wutar lantarki na Abuja DISCO a karshen mako ya bayyana cewa magance matsalar wutar lantarki a kasar nan ba abu ne mai yiwu ba a yanzu musamman saboda matsalar aiki da tsoffin kayan aiki da kamfanonin bayar da wutan keyi.

Babban daraktan kamfanin na Abuja DISCO, Ernest Mukwoya ne ya fadi wannan maganar a lokacin da yake jawabi a wani taron kaddamar da wata mujalla a Minna, mai taken ‘ Power Update Magazine.’

KU KARANTA:Wani mutum ya nemi kotu ta raba shi da masifaffiyar matarsa

A cewar daraktan, kamfaninmu ya gaji tsoffin kayayyakin aiki daga hannun tsohon kamfanin PHCN, wannan dalilin ne ya hana mu cin riba cikin wannan harkar tun lokacin da muka karbi kamfanin shekaru biyar da suka wuce.

Babban daraktan wanda ya samu wakilcin Janar Manaja na kamfanin, Israel Fadipe, ya ce: “ Kayan aikin da muke amfani da su a yau sun tsufa kwarai da gaske. Sun kai kimanin shekaru 115 ana amfani dasu,kafin mu samu damar sauya wadannan kayan muna buqatar kudi da kuma lokaci saboda sha’anin lantarki nada cin kudi sosai.

“ Gaskiyar lamarin dai shi ne, idan muka fitar da kudinmu bamu samun riba daga bangaren kwastamominmu.”

Har ila yau, yayi korafi kan masu sace kayan wuta da kuma wadanda basu ma biyan kudin wutan, inda yake cewa duk suna cikin dalilin da ya hana kamfanin nasu cigaba.

Bugu da kari, Daraktan ya sake fadin cewa kamfanin Abuja DISCO ya kashe naira biliyan goma domin sayen mita wadda ake sanya wa kati, amma kawo wa yanzu guda 300,000 kawai aka kawo masu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel