Hajjin bana: A yau ne za’a soma jigilar maniyyatan Najeriya zuwa Saudiya

Hajjin bana: A yau ne za’a soma jigilar maniyyatan Najeriya zuwa Saudiya

-Hukumar aikin hajji ta Najeriya ta bayyana ranar da za ta fara jigilar maniyyata zuwa kasa mai tsarki

-Gabanin tashi maniyyatan akwai tawagar farko mai dauke da jami'an hukumar NAHCON su 39 wadanda suka riga suka tafi tun Juma'ar da ta gabata

-Dr Kana Ibrahim ne ya bamu wannan labarin a hirarsa da gidan rediyo Freedom na jihar Kaduna a jiya Talata

A yau Laraba 10 ga watan Yuli ne za a fara jigilar maniyyatan Najeriya zuwa kasar Saudiya domin gudanar da aikin hajjin shekarar 2019, maniyyatan da zasu fara tashi sun fito ne daga Jihar Katsina.

Tawagar farko mai kunshe da jami’ai 39 na hukumar aikin hajjin Najeriya wato NAHCON sun isa kasar ta Saudiya tun a ranar Juma’ar da ta gabata.

KU KARANTA:Kada ku raina kasar Afirka ta Kudu, an gargadi Super Eagles

Shugaban hukumar ta NAHCON, Abdullahi Mukhtar Muhammad ne tare da tawagarsa suka raka maniyyatan har zuwa filin sauka da tashin jiragen sama na Nnamdi Azikiwe dake Abuja.

Har ila yau, akwai tawagar malaman kula da lafiya mutum 15 wanda Dr Ibrahim Kana ke jagoranta sun riga da sun isa kasar ta Saudiya.

Bugu da kari, duk daga cikin tsare-tsaren NAHCON a ko wane otal da maniyyatan Najeriyan zasu sauka akwai jami’i guda daya wanda zai kula da al’umaran masaukin nasu.

Haka zalika, NAHCON ta tanadi dakin bayar da agajin gaggawa musamman saboda lalurar rashin lafiya da kan iya faruwa a ko wane lokaci.

Shugaban tawagar malaman lafiyan da hukumar NAHCON ta aika Saudiya, Dr Kana shi ne ya bayyana mana wannan labarin a hirar da yayi jiya da gidan rediyon Freedom na Kaduna a cikin shirin Barka da Warhaka.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel