Nadin ministoci: Ba mu zamu sanya wa Buhari ranar fidda sunaye ba – Majalisar dattawa

Nadin ministoci: Ba mu zamu sanya wa Buhari ranar fidda sunaye ba – Majalisar dattawa

-Majalisar dattawa ta ce ba ta da ikon sanya baki cikin maganar sunayen sabbin ministocin da Shugaba Buhari zai nada

-Sanata Adeyeye ya mana fashin baqi kan wannan lamarin inda yake cewa doka ta bai wa Shugaban kasa damar yin wannan nadin a lokacin da ya so a don haka ba haqqin majalisa bane

-Majalisar dattawan na dab da tafiya hutu ba tare da sunayen ministoci ya iso gabanta ba

Majalisar dattawa a jiya Talata ta fadi cewa bata da hurumin cewa uffan dangane da yaushe ne Shugaba Muhammadu Buhari zai kawo sunayen ministocinsa majalisar domin a tantancesu.

Tun bayan rantsar da shi a karo na biyu wanda aka yi a ranar 29 ga watan Mayu da kuma kaddamar da sabuwar Majalisar dokoki a ranar 11 ga watan Yuni, yan Najeriya sun zuba ido domin ganin sunayen wadanda Shugaban kasan zai kai majalisa a matsayin ministocinsa.

KU KARANTA:Kada ku raina kasar Afirka ta Kudu, an gargadi Super Eagles

Da ake tambayarsa jiya kan wannan batu, shugaban kwamitin sadarwa da yada labarai na majalisar dattawan, Sanata Adebayo Adeyeye (APC, Ekiti) ya shaidawa wakilin Daily Trust na majalisar dattawan yadda lamarin yake.

Sanatan ya ce, haqqin Shugaban kasa ya zabi wadanda yake so a matsayin yan majalisarsa ta zartarwa saboda haka doka ta ba shi dama.

Kamar yadda Adeyeye ya sake cewa: “ Majalisar dattawa bata da ikon cewa uffan ga Shugaban kasa a kan nadin ministocin ko kuma ta ce ga wanda take so a ba wa.”

Da aka tambaye shi kuwa, shin bai ganin kamar jinkirin fitar da sunayen ministocin yayi tsawo sosai, ga amsar da ya bada: “ A’a sam ni ban ganin hakan, Shugaban kasa ne zai aiko da sunayen majalisarmu, kuma zai yi hakan a lokacin da ya ga dama, ni a ganina ba a bin damuwa bane wannan.

“ Majalisar dattawa na da na ta jadawalin, kwanan nan zamu tafi hutu kuma ko shakka babu bangaren zartarwa ya san da batun hutun namu.” A cewar sanatan.

Idan baku manta ba, Shugaban kasa ya dauki tsawon watanni biyu a wa’adinsa na farko kan ya nada ministoci bayan da ya lashe zaben 2015.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel