Dan Majalisa ya yi magana kan kutsen da 'Yan Shi'a su kayi a NASS

Dan Majalisa ya yi magana kan kutsen da 'Yan Shi'a su kayi a NASS

Dan Majalisar Wakilai na Tarayya, Abdulrazak Namdas (APC Adamawa) ya yi tir da kutsen da 'yan Shi'a su kayi zuwa cikin harambar Majalisar Tarayya da ke Abuja yayin zanga-zangar da su kayi a ranar Talata.

Namdas wanda mamba ne na kwamitin wucin gadi kan kafafen yada labarai ya yi alla wadai da kusten da akayi yayin wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN) a Abuja.

"Munyi alla wadai da abinda ya faru," Namdas ya shaidawa NAN.

DUBA WANNAN: Jerin sunaye: Mutum 5 da suka mallaki arzikin da ya fi kasafin kudin Najeriya

Da farko, 'yan kungiyar ta Islamic Movement of Nigeria da akafi sani da Shi'a sun shiga harabar majalisar ne inda suke bukatar a saki shugaban kasa Ibrahim El Zakzaky.

Masu zanga-zanga sun balle kofar farko na shiga majalisar inda suka yi arangama da jami'an tsaro.

Masu zanga-zangar sun rika amfani da duwatsu da sanduna suna jifar 'yan sanda da motocin farar hula da ke harabar inda suka fasa gilasan dakin masu tsaro majalisar.

Wasu 'yan sanda sun jikkata sakamakon arangamar kuma an garzaya da su asibitin da ke harabar majalisar domin yi musu magani.

An samu hargitsi a majalisar inda ma'aikata da wadanda suka kai ziyara suka rika tserewa domin tsira da lafiyarsu.

Kakakin Majalisar, Femi Gbjabiamila ya dage zaman majalisar cikin gaggawa saboda dalilan tsaro kamar yadda NAN ta ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel