Honarabul Emeka Martins ya cancanci yin takara inji Babban Kotun Najeriya

Honarabul Emeka Martins ya cancanci yin takara inji Babban Kotun Najeriya

Mun samu labari cewa babban kotun kolin Najeriya,ya yi watsi da karar da a ka kawo na ‘Dan majalisar tarayya mai wakiltar yankin mazabar Ahiazu da Ezinihitte watau Emeka Martins.

Idan ba ku manta ba, a na zargin Honarabul Emeka Martins da laifin yi wa hukuma karya a game da takardun da ya gabatarwa hukumar zabe na kasa lokacin da ya ke neman takarar ‘dan majalisa.

Alkalan kotun kolin a karkashin jagorancin mai shari’a Bode Rhodes-Vivour, sun yi fatali da karar da a ka daukaka zuwa gabansu. Alkali Rhodes-Vivour ya yanke hukuncin a yi fatali da shari’ar.

Kamar yadda mu ka samu labari daga Premium Times a Ranar 8 ga Watan Yuli, 2019, Alkalai 5 ne su ka zauna su ka yanke wannan hukunci inda su ka ce Emeka Martins ya cancanci ya rike ofis.

KU KARANTA: Da dole a ka sa ni na sa hannu a kan takardun zaben 2019 – Inji Shaidan PDP

Wani Lauya, Nnanna Igbokwe ya na zargin ‘dan majalisar da mikawa hukumar INEC takardun jabu a fam din sa na CF 001. A dalilin haka ya nemi a ruguza takarar da yayi a zaben 2019.

Emeka Martins ya yi magana bayan nasarar da ya samu a kotu inda ya ce Jama’a ba su da gatar da ta wuce gaban kuliya. Ya ce: “Ta tabbata Alkalai su na zaman kan-su ne ba na kowa ba, a kasar nan.”

‘Dan majalisar ya ke kuma cewa: “Na ji dadin yadda a ka yi watsi da wannan kara. Wannan shari’a ta nuna cewa babu wanda zai iya yi wa bangaren shari’a katsalandan, kuma wannan a ke bukata.”

Kafin nan an samu kotun da ya ba N. Igbokwe rashin gaskiya kwanaki a wannan shari’a. Daga baya ya daukaka kara zuwa babban kotu, har maganar ta kai gaban babban kotun kolin Najeriya.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel