Dalilai 4 da zasu sa kotu ta yanke wa sanata Abbo hukuncin daurin shekaru 3 a gidan yari

Dalilai 4 da zasu sa kotu ta yanke wa sanata Abbo hukuncin daurin shekaru 3 a gidan yari

A yayin da kotu ta bayar da belin sanata Elisha Abbo bayan rundunar 'yan sanda ta gurfanar da shi bisa tuhumarsa da laifin cin zarafin wata matar aure a wani shagon sayar da kayan batsa da ke Abuja, masana shari'a sun yi nazarin wasu dalilai biyar da idan kotu ta yi la'akari da su, za ta iya yankewa Sanatan daurin shekaru uku.

1. Abbo ya saba wa kundin manyan laifuka na Najeriya kamar yadda ya ke a cikin sura ta 29, aya ta 351 da ta 355 wadanda suka yi magana a kan cin zarafi da kuma hukuncin daurin shekara daya a gidan yari ga duk wanda aka samu da laifin aikata hakan.

2. Na biyu, laifin da ake tuhumar Abbo da aikata wa ya saba wa dokar majalisar dinkin duniya (UN) a kan cin zarafin mata da kasashen duniya da suka hada da Najeriya suka rattaba hannu a kan ta. Duk da UN ba ta tilasta kasashe yin amfani da dokar cin zarafi ba, kasashe da dama na yin amfani da ita domin kare hakkin bil'adama.

DUBA WANNAN: Yadda wata matashiya mai shekaru 14 ta hada baki da saurayinta suka kashe yayan ta

3. Dalili na uku da masana shari'a suka bayyana shine batun afuwar da Sanatan ya nema. Masu wannan ra'ayi na ganin cewa bai kamata a kyale sanata Abbo ba duk da ya fito fili ya nuna ya yi nadama, saboda, a cewarsu, hakan kan iya bude kafar cin zarafin mata sannan daga baya a bayar da hakuri.

Masu wannan ra'ayi sun nuna shakku a kan nadamar sanata Abbo, su na masu bayyana cewar tamkar ma an lallabe shi ne domin ya bayar da hakuri, saboda a karon farko ya nemi ya nuna cewa bidiyon tsoho ne, kafin daga bisani ya jingine wannan batu tare da bayar da hakuri a wani salo kamar na shirin fim.

4. Wani bangare na masu rajin kare hakkin bil'adama, musamman masu kare hakkin mata, sun bayyana cewa ana yawan samun matsalar cin zarafin mata a Najeriya ba tare da ana daukan wani mataki ba, hasali ma ba kasafai ake yada irin cin zarafin da ake yi wa matan ba ko kuma rashin hujja yasa a kasa hukunta wanda ya ci zarafin mace idan ma an ki shi kotu.

Kungiyoyin na son ganin an hukunta sanata Abbo, musamman idan aka yi la'akari da cewa an nadi faifain bidiyonsa yayin da yake marin matar a cikin shagon.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel