Ba dole bane sai dan kudu ya zama shugaban kasa - Jigo a APC

Ba dole bane sai dan kudu ya zama shugaban kasa - Jigo a APC

Sakataren tsare-tsare na kasa na jam'iyyar APC kuma jigo daga yankin Kudu Maso Gabashin kasar nan, Barrister Emma Ibediro ya ce neman kujerar shugaban kasa da 'yan kabilar Ibo ke yi kuskure ne.

A hirar da ya yi da manema labarai ranar Talata a Abuja, Barr. Ibediro ya ce hanyar daya da 'yan Ibo za su bi wurin fitar da dan takarar shugaban kasa shine idan masu ruwa da tsaki daga yankin da ke APC sun gamsar da sauran 'yan Najeriya.

"Ba dole bane a bawa Ibo shugabancin kasa kamar yadda yake ba dole bane a bawa bahaushe. Suma Yarabawa ba dole bane a basu. Za a iya samun shugaban kasa Ibo ne kawai idan 'yan jam'iyyar sun gamsar da sauran 'yan Najeriya.

DUBA WANNAN: Jerin sunaye: Mutum 5 da suka mallaki arzikin da ya fi kasafin kudin Najeriya

"Saboda haka idan mutanen Kudu Maso Gabas suna son samar da shugaban kasa, ina ganin abinda ya dace shine su fara aiki a jam'iyya sannan su gamsar da 'yan Najeriya. Ba wai dole ne ba. Wannan shine abinda zan fadi," inji shi.

Jigon na APC ya kuma ce baya goyon bayan wai dole sai jam'iyyar ta bawa dan Kudu takarar shugabancin kasa saboda a gina jam'iyyar kan kama karya ba.

Ya ce ya zama dole mutanen Kudu Maso Gabas suyi siyasar cudanya da hadin kai da sauran yankunan Najeriya inda ya ce a yanzu, "Bana tunanin muna irin wannan siyasar ta cudanya da sauran mutane."

Ibediro ya cigaba da cewa siyasa, "cuda ni in cuda ka ne. Ni mutumin kudi ne kuma ya zama dole in fadi gaskiya. Shugaban kasa ya yi kamfe da dukkan jihohi 5 na Kudu maso Gabas amma bai samu wasu kuri'u na azo a gani ba. Ba zai yiwu ka nemi a baka wani abu yayin da kai ba za ka bayar da komi ba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel