Mataimakin shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo, ya fito ya koka da yadda wasu daga cikin ‘yan siyasan kasar nan su ke amfani da rikicin addini da kabilanci da a ke yawan fama da shi.
Yemi Osinbajo ya ke cewa manyan ‘yan siyasa ne su ka jawo a ka gaza samun zaman lafiya. Osinbajo ya ce ‘yan siyasa na cin galabar bakar tsanar da ke yawo a cikin zukatun jama’a.
Farfesa ya yi wannan bayani ne a lokacin da ya ke jawabi wajen bikin taya tsohon gwamnan jihar Ogun, Olusegun Osoba murnar cika shekara 80 a Duniya inda a ka kaddamar da littafin tarihinsa.
Osinbajo ya ce daga cikin rikicin da ‘yan siyasa su ka jefa kasar nan shi ne jawo rashin yadda da jituwa a tsakanin mutane. Osinbajo ya ce akwai bukatar a kawo karshen irin wannan matsalar.
KU KARANTA: An damke 'Yan Shi'a 40 bayan rikicin da a ka yi a Majalisa
Mataimakin shugaban kasar ya ce a na cin moriyar sabanin addini da kabilancin da a ka samu, wanda a cewar sa hakan ba karamin hadari ba ne inda ya nemi a yi maganin wannan mugun nufi.
Tsohon Sakataren gwamnatin Najeriya, Babagana Kingibe, a na sa jawabin, ya nuna cewa babu wani bangaren Najeriya da bai da amfani don haka ya nemi kaf mutanen kasar su hada-kan su.
Manyan ‘yan siyasa irin su jigon jam’iyyar APC watau Asiwaju Bola Tinubu sun halarci wani taron da tsohon shugaban kasa Janar Abdussalami Abubakar ya jagoranta a karshen makon nan.
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan