Dan majalisa ya caccaki yan Shi’a saboda afka ma a majalisar dokokin Najeriya

Dan majalisa ya caccaki yan Shi’a saboda afka ma a majalisar dokokin Najeriya

Dan majalisar wakilai daga jahar Adamawa, Abdulrazak Namdas ya caccaki lamirin mabiya addinin Shia tare da yin Allah wadai bisa kutsen da suka yi ma majalisar dokokin Najeriya a ranar Talata, 9 ga watan Yuli, inji rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Namdas ya bayyana haka ne yayin da yake tattaunawa da ita a garin Abuja bayan kura ta lafa a majalisar, biyo bayan rikicin daya auku tsakanin Yansanda da yan Shia da rana.

KU KARANTA: Yawan kisan kai a Najeriya: Sanatoci sun nemi a hana sayar da ‘Sniper’ a kasuwa

Dan majalisa Namdas yace: “Majalisa ta yi tir da Allah wadai da matakin da yan Shia suka dauka na afka ma majalisar.” Da fari yan Shia sun gudanar da zanga zanga ne a babban birnin tarayya Abuja, inda suka yi tattaki zuwa majalisar dokokin Najeriya.

Yan Shian suna zanga zangar ne don nuna bacin ransu ga cigaba da tsare shugabansu Ibrahim Zakzaky da gwamnatin tarayya ke yi, tare da bukatar shugaban kasa Buhari ya sako musu shi cikin gaggawa.

A yayin wannan zanga zanga ne yan Shian suka balla kofar shiga majalisar ta farko wanda hakan tasa suka yi fito na fito da jami’an tsaro, har ta kai ga yan shi’an sun yi amfani da duwatsu da katako wajen farfasa motocin mutane da gilasan tagogin ofishin jami’an tsaron majalisar.

Mutane da dama daga bangaren yan shi’an zuwa na jami’an tsaro sun samu munanan rauni, yayin da jama’an garin Abuja suka shiga halin dimuwa da firgici, kowa ya yi ta gudu.

Daga karshe dai kaakakin majalisar, Femi Gbajabiamila ya dage zaman majalisar ba shiri, inda ya danganta hakan ga matsalar tsaro a farfajiyar majalisar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel