Yan sanda sun damke mana mutane kusan 100 – Kungiyar Shi’a

Yan sanda sun damke mana mutane kusan 100 – Kungiyar Shi’a

A yau Talata, 9 ga watan Yuli ne aka yi bata-kashi tsakanin jami’an yan sanda da mambobin kungiyar shi’a da ke zanga-zangar a saki shugabansu a harabar majalisar dokokin tarayya.

Lamarin ya haddasa gagarumin tashin hankali a majalisar dokokin kasar sakamakon barin wuta da akayi wanda yayi sanadiyar harbin wasu jami’an yan sanda, inda daya daga cikinsu ya mutu a nan take.

Hakan yayi sanadiyar kama wasu daga cikin mabiya shi’a, inda rundunar yan sanda ta sanar da kama mambobin kungiyar 40.

Sai dai kuma, Muhammad Ibrahim Gamawa, daya daga cikin masu magana da yawun kungiyar ya musanta zarge-zargen 'yan sandan, inda ya ce ba su da makaman da 'yan sandan suka ce sun yi harbi da su.

Ya kuma kara da cewa sabanin mutum 40 da rundunar 'yan sandan ta ce ta kama musu, an "kama mana kusan mutum 100."

'Yan Shi'ar dai sun ce suna zanga-zanga ne kan ci gaba da tsare jagoransu Sheikh Ibrahim Elzakzaky da gwamnati ke yi wanda suka ya ce "yana cikin mummunan yanayin rashin lafiya".

KU KARANTA KUMA: Yawan kisan kai a Najeriya: Sanatoci sun nemi a hana sayar da ‘Sniper’ a kasuwa

A halin da ake ciki mun ji cewa, Dan majalisar wakilai daga jahar Adamawa, Abdulrazak Namdas ya caccaki lamirin mabiya addinin Shia tare da yin Allah wadai bisa kutsen da suka yi ma majalisar dokokin Najeriya a ranar Talata, 9 ga watan Yuli, inji rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Namdas ya bayyana haka ne yayin da yake tattaunawa da ita a garin Abuja bayan kura ta lafa a majalisar, biyo bayan rikicin daya auku tsakanin Yansanda da yan Shia da rana.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel