Cin zarafin matar Aure: Sanata Elisha Abbo ya gurfana gaban majalisa

Cin zarafin matar Aure: Sanata Elisha Abbo ya gurfana gaban majalisa

Sanatan majalisar dattawa, Elisha Abbo, wanda aka kama a faifan bidiyo yana cin zarafin wata matar aure a shagon kayan jima'i ya gurfana gaban kwamitin majalisar dattawa da aka kafa musamman domin bincikensa.

Abbo ya gurfana gaban kwamitin ne a ranar Talata, 9 ga watan Yuli, 2019.

Sanatan mai wakiltar mazabar Adamawa ta Arewa ya ki rantsewa gaban kwamitin kuma ya ce ba zai fadi komai gaban yan jarida ba.

A tarihin majalisa, duk wanda ya gurfana gaban kwamirin bincike sai ya rantse da littafin da yayi imani da shi kafin yayi magana.

Hakan ya jawo mujadala tsakaninsa da mambobin kwamitin yayinda suka ce wajibi ne ya rantse kuma amma ya lashi takobin cewa ba zai rantse ba.

Wata Mambar kwamitin, Oluremi Tinubu, ta bukaci Abbo ya rantse kafin ya furta kalma daya saboda suna da damar dakatad da shi daga shiga majalisa

Tace: "Sanata, kai sabon zuwa ne. Muna da ka'ida kuma muna da doka. Ba zaka shigo nan ka fada mana abinda abinda zamu yi ba. Za mu iya dakatad da kai."

Sanata Abbo yace: "Wannan al'amari na kotu. Ba zai yiwu in rika magana gaban yan jaridar kan al'amarin da ke kotu ba."

"Ba zan zauna a nan kina yi min barazanar dakatad da ni ba. Ni sanata ne kamar ki. Baki isa ki yi mini barazana ba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel