Shari’ar zabe: Buhari ya ki amincewa a gabatar da takardun ilmin sa a kotu

Shari’ar zabe: Buhari ya ki amincewa a gabatar da takardun ilmin sa a kotu

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ki yarda a yi amfani da bayanan takardun makarantar sa a kotun daukaka karar zaben shugaban kasa, jaridar Premium Times ta ruwaito.

Babban Lauyan Buhari, Wole Olanipekun ne ya nuna kin amincewar a ranar Litinin, 8 ga watan Yuli yayinda ake ci gaba da sauraron karar zaben nasa, wadda Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da dan takara ta, Alhaji Atiku Abubakar ya suka kai kotu.

Daga cikin abin da PDP za ta gabatar wa kotu, har da takardun bayanan iya zurfin ilmin da Buhari ya hada a cikin fam din INEC mai lamba CF001, wanda jam’iyyar adawa ke kalubalantar cewa babu wasu takardun kammala shaidar karatun sakandare na Shugaban kasar.

Har ila yau daga cikin hujjojin rashin cancantar sa tsayawa takarar da PDP da Atiku ke tinkaho dashi, sun hada da abin da wannan fam mai lamba CF001 ya kunsa.

Shi wannan fam duk bayanan da ke cikin sa, da kuma takardun da aka hada aka bayar wa INEC tare da shi, da su ne ake tabbatar da cancantar tsayawa takara, ko kuma rashin cancantar tsayawar dan takara zabe.

KU KARANTA KUMA: Na yi danasanin rashin mika mulki ga dan takarar da na so – Tsohon gwamna Yari

Jam’iyyar APC wadda Buhari ya tsaya takara a karkashin ta, ta ki amincewa da a gabatar da batun fam CF001 a kotun daukaka Kararrakin zabe, ta bayyana wa Alkalai masu shari’a cewa za ta fadi dalilan ta na kin amincewa da batun.

Sauran takardun bayanan da aka gabatar wa kotu a matsayin shaidu a jiya Litinin, har da kwafe-kwafen wasu bayanai da aka buga a wasu jaridun kasar nan, sai kuma kwafe-kwafen takardun sakamakon zabe.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel