Ku yi watsi da zancen: Buhari bai nada sabon hafsan rundunar soji ba - Rundunar soji

Ku yi watsi da zancen: Buhari bai nada sabon hafsan rundunar soji ba - Rundunar soji

Rundunar soji ta kasa (NA) ta ce babu gaskiya a cikin wasu rahotanni da ke yawo a kafafen yada labarai da na sada zumunta a kan cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya canja shugaban rundunar soji, Laftanal Janar Tukur Buratai.

A ranar Talata ne shugaba Buhari ya amince da kara wa Manjo Janar Lamidi Adeosun mukami zuwa Laftanal Janar, mukamin Buratai. Jim kadan bayan sanarwar hakan ta fita sai wani bangare na kafafen yada labari suka wallafa labarin cewa Buhari ya maye gurbin Buratai da Adeosun.

Sai dai, a wani jawabi da kakakin rundunar soji ta kasa, Kanal Sagir Musa, ya fitar, ya bayyana labarin da cewa 'shaci fadi' ne kawai, sannan ya kara da cewa har yanzu Adeosun na nan a kan mukaminsa na shugaban sashen horo da atisaye a hedikwatar rundunar soji ta kasa.

Ya ce, "ku yi watsi da labarin 'kanzon kuregen' da ke yawo a gari a kan cewa Laftanal Janar L.O Adeosun ya zama sabon shugaban rundunar soji ta kasa.

DUBA WANNAN: Yadda wata matashiya mai shekaru 14 ta hada baki da saurayinta suka kashe yayan ta

"Mu na kira ga jama'a da su yi watsi da wannan labari, tare da sanar da su cewa Laftanal Janar Adeosun ya samu karin girma na musamman ne, kuma babban hafsan rundunar soji, Laftanal Janar T. Y Buratai, ne ya sanar da shi karin girman da aka yi masa.

"Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ne ya yi masa karin girma na musamma saboda kwazonsa da jajircewa a kan aiki da kuma irin gudunmawar da ya bayar a yaki da ta'addanci a yankin arewa maso gabas.

"Hakan ba yana nufin cewa an nada shi a matsayin sabon shugaban rundunar soji ba ne, har yanzu yana nan a kan mukaminsa na shugaban sashen bayar da horo da atisaye a hedikwatar rundunar soji ta kasa."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel