Kuma dai: Kotu ta kwace filin Diezani ta mika wa Gwamnatin Tarayya

Kuma dai: Kotu ta kwace filin Diezani ta mika wa Gwamnatin Tarayya

Babban Kotun Tarayya da ke zamanta a Legas, a ranar Talata ta bayar da umurnin mika wa gwamnatin tarayya wasu filaye mallakar tsohuwar Ministan Albarkatun Man Fetur, Mrs Diezani Alison-Madueke da ke Fatakwal a jihar Rivers.

Justice Chuka Obiozor ne ya bayar da wannan umurnin bayan wata kara da Hukumar Yaki da Rashawa EFCC ta shigar a kotun.

Hukumar Yaki Da Rashawar ta fadawa alkali cewa, "An zargin filin mai fadin sakwaya mita 7,903.71 – 8,029.585 mai suna Plot 9 Azikwe Road, Old GRA a Fatakwal an mallake shi ne ta bayan fage.

DUBA WANNAN: Shaidan Atiku da PDP ya basu kunya a gaban kotu

Hukumar ta kuma roki kotu ta ba ta izini ta nada kwararen jami'i da zai kula da filin."

Ta bukaci kotu ta hana sayar da filin ko bayar da shi haya ko wani abu mai alaka da hakan.

Lauyan EFCC, Ebuka Okongwu ya ce alkalin kotun a karkashin sashi na 17 na dokar masu damfara da laifuka masu alaka da damfara ta 2006 ya kwace filin.

Bayan sauraron lauyan, Justice Obiozor ya bayar da umurnin kwace filin kamar yadda lauyan ya nema.

A ranar Juma'a da ta gabata, Babban Kotun Tarayya ta bayar da umurnin kwace gwalagwalai mallakar Diezani da wayar salula kirar iPhone na gwal wanda kudinsu ya kai dallar Amurka miliyan 40.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel