Mun damke yan Shi'a 40 - Kakakin hukumar yan sanda

Mun damke yan Shi'a 40 - Kakakin hukumar yan sanda

Hukumar yan sandan Najeriya a ranar Talata ta bayyana cewa yan kungiyar mabiya akidar Shi'a sun harbe hafsoshin yan sanda biyu.

Mun kawo muku rahoton cewa yan Shi'a sun je zanga-zanga majalisar dokokin tarayya amma abin yayi muni daga baya.

Yan Shi'a suna gudanar da zanga-zangan bukatar gwamnatin tarayya ta saki jagoransu, Sheikh Ibrahim Zakzaky wanda ya kasance hannun hukumar tun watan Disamban 2015. Akalla yan Shi'a 340 aka kashe lokacin da soji suka kai farmaki cibiyar Shi'a dake Zariya.

A ranar Talata, kakakin hukumar yan sandan Abuja, Anjuguri Manzah, ya ce sun damke akalla yan Shi'a 40.

KU KARANTA: Daya daga cikin yan sandan da yan Shi'a suka harba, Umar Abdullahi, ya kwanta dama

Yace: "Hukumar yan sandan birnin tarayya a dakile wani yunkuri da mambobin kungiyar El-Zakzaky sukayi na shiga majalisar dokokin tarayya ranar Talata, 10 ga watan Yuli, 2019."

"Mambobin kungiyar sun harbe jami'an yan sanda biyu a kafa, yayinda suka jikkata wasu yan sanda shida ta hanayr jifa da duka. An garzaya da yan sandan asibiti domin jinya."

"Amma mun damke yan Shi'a 40 da sukayi wannan zanga-zanga kuma ana gudanar da bincike."

Mun kawo rahoton cewa daya daga cikin jami'an yan sanda hudu da yan kungiyar Shi'a suka lallasa, Umar Abdullahi, a majalisar dokokin tarayya ya rigamu gidan gaskiya.

Sauran da suka rage yanzu sune DPO na majalisa wanda aka cakawa wuka, da wasu hafsoshi biyu, kuma suna asibiti.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel