Dalilin da ya sa nake son zama gwamnan jihar Kogi - Dino Melaye

Dalilin da ya sa nake son zama gwamnan jihar Kogi - Dino Melaye

Daya daga cikin shahararrun 'yan majalisar dattawan kasar nan, Sanata Dino Melaye, ya fayyace babban dalilin da ya sanya yake matukar muradin zama gwamnan mahaifar sa da ta kasance jihar Kogi.

Sanata Dino Melaye, wanda tuni ya bayyana kudirin tsayawa takarar kujerar gwamnatin jihar Kogi, ya bayyana dalilan sa na kasancewa gwamnan jihar Kogi a cikin wani faifan bidiyo da ya yada a shafin sa na zauren sada zumunta.

Cikin faifan bidiyon, Dino Melaye mai wakilcin shiyyar Kogi ta Yamma a zauren majalisar dattawan kasar nan karkashin inuwa ta jam'iyyar APC, ya ce babban dalilin sa na son zama gwamnan jihar Kogi bai wuci muradin sa na tsamo ta daga kangin da take ciki a yanzu.

KARANTA KUMA: Rikicin kabila: 'Karancin abinci zai mamaye jihar Taraba

Sanatan ya wassafa halin kunci da jihar Kogi ke ciki kama daga rashin biyan albashi, yunwa, rashin tsaro, ta'addancin masu garkuwa da mutane,cin zarafin kananan yara da sauran munana ababe masu dakile ci gaban al'umma.

A wani rahoton mai nasaba da wannan jaridar Legit.ng ta ruwaito, tsohon gwamnan jihar Bayelsa, Timipre Sylva, ya daura kunzugunsa na dawowa kujerar gwamnati yayin zaben gwamnan jihar da za a gudanar a watan Fabrairun 2020.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel