Zaben Gwamna: APC zata gudanar da zaben fidda gwani a jihohin Bayelsa da Kogi ranar 29 ga watan Agusta

Zaben Gwamna: APC zata gudanar da zaben fidda gwani a jihohin Bayelsa da Kogi ranar 29 ga watan Agusta

-Jam'iyyar APC ta fadi ranar da zata gudanar da zaben fidda a gwani a jihohin Bayelsa da Kogi

-Duk a cikin wannan labari jam'iyyar ta bayyana kudin da ko wane dan takara zai biya domin sayen fom din tsayawa takara

-Bayan kammala zaben firamare na fidda gwani jam'iyyar ta fadi ranar 2 ga watan Satumba a matsayin ranar da zata saurari korafe-korafe a kan zaben

Jam’iyyar APC ta sanya ranar Alhamis 29 ga watan Agusta a matsayin ranar da za ta gudanar da zaben fidda gwani a jihohin Bayelsa da Kogi domin zaben gwamnan dake tafe ranar 16 ga watan Nuwamba a jihohin biyu.

Jam’iyyar har wa yau, ta sanar cewa zata fara sayar da fom ga ‘yan takara a ranar Laraba 10 ga watan Yuli, 2019 a babban ofishinta na kasa dake Abuja.

KU KARANTA:Da zafinsa: ‘Yan majalisa 14 na Edo sun tunkari Majalisar dokoki da neman a sake zaben shugabancin majalisar jiharsu

Babban sakataren tsare-tsare na jam’iyyar, Emma Ibediro ya bayyana cewa duk wanda ke sha’awar tsayawa takarar zai kashe miliyan N22.5.

Ibediro ya cigaba da cewa, “idan kuwa aka samu ‘yar takara mace ko kuma namiji amma wanda keda wata nakasa daga jikinsa zai biya 50% na kudin da na ambata a farko ne kacal.”

Majiyar jaridar The Nation ta sanar damu cewa za’a kulle sayar da fom din ne a ranar Talata 20 ga watan Agusta yayin da maido da fom din bayan an cika kuma za’a rufe shi ranar Laraba 21 ga watan Agusta.

Haka zalika, jam’iyyar ta sake fadin ranar da zata tantance ‘yan takarkarun jihohin biyu, ranar Alhamis 22 ga watan Agusta ita ce ranar tantance yan takarar, inda za’a saurari korafe-korafe kan tantancewar a ranar Juma’a 23 ga watan Agusta. Sai kuma abu na karshe wanda shi ne korafe-korafe daga zaben firamare wanda zai kama ranar Litinin 2 ga watan Satumba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel