Yadda wata matashiya mai shekaru 14 ta hada baki da saurayinta suka kashe yayan ta

Yadda wata matashiya mai shekaru 14 ta hada baki da saurayinta suka kashe yayan ta

Jami'an tsaro sun kama wata yarinya mai shekaru 14 tare da saurayinta ranar Lahadi a birnin Taiping na ksar Malaysia bisa zarginsu da kashe yayan matashiyar, wanda aka bayyana cewa ya bata ranar Juma'a.

An tsinci gawar yayan yarinyar da misalin karfe 12:18 na ranar Lahadi a kunshe a cikin wata jakar leda a wani gida da ke unguwar Taman Glenview a yankin Kamunting.

Mataimakin kwamishinan 'yan sanda a birnin Taiping, Osman Mamat, ya ce iayeyn matashiyar sun shigar da korafin batan yayan ta ranar Juma'a bayan basu ga dawowarsa daga makaranta ba ranar Juma'a.

A ranar Litinin ne da misalin karfe 4:25 na yamma jami'an 'yan sanda suka kama matashiyar da saurayinta mai shekaru 15 bayan an gano gawar yayan na ta.

"Da suke amsa tambayoyi, matasan sun amsa da bakinsu cewar su ne suka kashe matashin," a cewar Mamat.

DUBA WANNAN: 'Shaci fadi' ne kawai: Buhari bai nada sabon hafsan rundunar soji ba - Rundunar soji

Da ya ke bayyana abinda matasan suka sanar da jami'an 'yan sanda, Mamat ya ce, "yarinyar ce ta gayyato saurayinta gidansu, shi kuma yayan ta hakan ya fusata shi har ta kai ga fada ya kaure a tsakaninsu, lamarin da ya kai ga budurwar da saurayinta sun yi wa mamacin taron dangi tare da ji masa rauni a wuya."

Mamat ya kara da cewa jami'an 'yan sanda sun fahimci cewa matasan sun yi amfani da wani abu mai karfi wajen yi wa marigayin rauni a wuya, wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwarsa.

An aika gawar marigayin zuwa asibitin Rsja Permaisuri Bainun da ke Ipoh domin gudanar da gwaje-gwajen gano musabbabin mutuwarsa.

Yadda wata matashiya mai shekaru 14 ta hada baki da saurayinta suka kashe yayan ta

Matashiya mai shekaru 14 da saurayin ta
Source: Facebook

Yadda wata matashiya mai shekaru 14 ta hada baki da saurayinta suka kashe yayan ta

Yadda wata matashiya mai shekaru 14 ta hada baki da saurayinta suka kashe yayan ta
Source: Facebook

Yadda wata matashiya mai shekaru 14 ta hada baki da saurayinta suka kashe yayan ta

Matashiya mai shekaru 14 ta hada baki da saurayinta sun kashe yayan ta
Source: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel