Yanzu-yanzu: Daya daga cikin yan sandan da yan Shi'a suka harba, Umar Abdullahi, ya kwanta dama

Yanzu-yanzu: Daya daga cikin yan sandan da yan Shi'a suka harba, Umar Abdullahi, ya kwanta dama

Labarin dake shigo mana da duminsa na nuna cewa daya daga cikin jami'an yan sanda hudu da yan kungiyar Shi'a suka lallasa, Umar Abdullahi, a majalisar dokokin tarayya ya rigamu gidan gaskiya.

Sauran da suka rage yanzu sune DPO na majalisa wanda aka cakawa wuka, da wasu hafsoshi biyu, kuma suna asibiti.

Mun samu labarin cewa yayinda aka harbi daya a hakarkari, a cinya aka harbi daya.

Yan kungiyar Shi'a biyu da aka kama zuwa yanzu suna shan tambayoyi a ofishin hukumar DSS a lokacin muke kawo wannan rahoto.

KU KARANTA: Yadda yan Shi'a suka farwa jama'a da jami'an tsaro a majalisar dokokin tarayya a Abuja (Hotuna da Bidiyo)

Ku saurari cikakken rahoton....

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel