Kada ku raina kasar Afirka ta Kudu, an gargadi Super Eagles

Kada ku raina kasar Afirka ta Kudu, an gargadi Super Eagles

-Masoya wasan kwallon kafa a Kaduna sun roki Super Eagles kan su doke Afirka ta Kudu domin matsawa mataki na gaba a gasar AFCON 2019

-Isiah Benjamin ya gargadin yan wasan na Super Eagles da cewa kada su raina yan wasan Afirka ta Kudu domin sun fi karfin raini a halin yanzu

-Akinbami ya bayyana ra'ayinsa inda ya ce shi nasara kawai yake hangowa a wannan wasa da za'a buga da Afirka ta Kudu

Masoya wasan kwallon kafa dake Kaduna sun roki ‘yan wasan Super Eagles da cewa suyi kokarin lashe wasan da za su kara da Afirka ta Kudu domin samun damar hayewa zuwa zagayen kusa da karshe.

Masoya wasan kwallon wadanda suka samu zantawa da kamfanin dillacin labaran Najeriya NAN sun ce, akwai buqatar ‘yan wasan Super Eagles su dauki wannan wasa da matuqar muhimmanci kuma su bugashi da gaske bada wasa ba.

KU KARANTA:Da zafinsa: ‘Yan majalisa 14 na Edo sun tunkari Majalisar dokoki da neman a sake zaben shugabancin majalisar jiharsu

Isaiah Benjamin wanda shi ne Shugaban marubatan labaran wasanni na Najeriya, reshen Jihar Kaduna, ya ce, duk da yake akwai batutuwa daban-daban dangane da wasan, idan har Super Eagles suka taka leda da kyau za su samu nasara.

Benjamin ya cigaba da cewa: “ Afirka ta Kudu ta fi karfin raini a wurin duk wanda zai kara da ita. Ya zama wajibi ga Super Eagles da su dage domin kai wa zuwa mataki na gaba.

“ Babu shakka wasannin na dada tsauri, amma da yadda nake ganin salon wasansu ina kyautata zaton za su doke Afirka ta Kudu.”

Wani masani wanda ke yin fashin baki a kan lamuran wasanni, Vincent Akinbami ya bayyana ra’ayinsa a fili inda yake cewa za’a samu nasara a wannan wasa.

Akinbami yana cewa: “ Da can abinda ke matsalar ‘yan wasan shi ne rashin buga wasa cikin tsari a mastayin tawaga guda. Amma yanzu abin ya sauya, da kuma ‘yan kasar Masar mai masauki baki wadanda za su goya mana baya, nasara tamu ce kawai.”

Source: Legit

Mailfire view pixel