Ba gudu ba ja da baya: Jihar Gombe na nan akan bakarta na gina Ruga – Inuwa Yahaya

Ba gudu ba ja da baya: Jihar Gombe na nan akan bakarta na gina Ruga – Inuwa Yahaya

Gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya, ya bayyana cewa gwamnatin sa ba za ta janye daga aikin gina ruga domin amfanin makiyaya ba a jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne bayan wata ganawa da ya yi tare da Shugaba Muhammadu Buhari Buhari a Fadar Shugaban Kasa.

Shirin gina rugage dai shiri ne da gwamnatin tarayya ta dauki kudirin ginawa makiyaya matsugunai domin daina yawace-yawacen zuwa kiwo wurare masu nisa.

Za a samar da ababen more rayuwa kamar kananan madatsun ruwa, asibitoci da makarantu da kuma kasuwanni. Hakazalika za a samar da asibitin dabbobi.

Amma dai kuma gwamnatin tarayya ta sanar da dakatar da shirin bayan kace-nace da aka dunga yi kan lamarin.

Sai dai kuma shi gwamnan Gombe, ya bayyana cewa, “a maganar nan da ke yi da ku yanzu, Gwamnatin Jiar Gombe ta kebe fili mai eka 200,000 domin aiwatar da shirin kafa rugagen Fulani makiyaya a jihar.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Yan Shi’a da ke zanga-zanga sun harbi yan sanda 3 a majalisar dokoki

“Don kawai wasu jihohi sun ki amincewa da shirin, hakan ba zai sa mu a jihar Gombe mu ki amincewa da shirin ba.

“Za su aiwatar da shirin, domin mu dai mu na ganin cewa zai zama alheri ga makiyaya, wadanda a halin yanzu ke faman wahalalhalun yawon kiwon dabbobin su.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel