Sanatoci sun yi kira da a samar da hukuncin kisa ga masu yi ma yara fyade

Sanatoci sun yi kira da a samar da hukuncin kisa ga masu yi ma yara fyade

-Sanata Tinubu da sanata Sekibo sun yi kira da a sanya hukuncin kisa ga masu yi ma kananan yara fyade

-Sanatocin sun bayyana haka ne a lokacin da sanata Okoh ya gabatar da wani kudiri akan irin yawan fyade da ake yi ma kananan yara a kasarnan

-Okoh ya bayyana cewa duk cikin yara 10 yan kasa da shekaru 18, shida daga ciki na fuskantar matsalar fyade

Sanata Oluremi Tinubu mai wakiltar Legas ta tsakiya da sanata Thompson Sekibo da ke wakiltar gabashin Rivers sun yi kira da a samar da hukuncin kisa ga masu yima yara fyde.

Sanatocin sun yi wannan kira ne a lokacin da suke bada gudunmuwa a kudirin da sanata Rose Okoh, sanata mai wakiltar arewacin Cross Rivers a yau Talata 9 ga watan Yuli 2019 ya gabatar. Oko ya jawo hankalin majalisar dattawa akan yawan fyade da ake yima yara a Najeriya.

Da take bada gudunmuwa a muhawarar, Tinubu ta bayyana cewa yara na cikin hadari saboda yadda ake yawan yi ma kananan yara fyde.

Ta bayyana cewa “Babban laifi ne kuma ina tunanin ya kamata a sanya mashi hukuncin kisa yanzu.”

“Mafi yawan masu aikata laifin suna aikata shi ne akan wadanda suke tare da su. Mafi yawancinsu yan uwa ne. Lokaci yayi da ya kamata muyi abun daya dace. Don magance wannan annoba.”

“Ya kamata a bawa iyaye horo akan yadda za su tarbiyyantar da yaransu. Ya kamata su wayar da kan ‘ya’yansu akan ilimin jima’i.”

KARANTA WANNAN: Rikicin kabila: 'Karancin abinci ya mamaye jihar Taraba

Da yake bayar da tashi gudunmuwar, Sekibo ya bayyana cewa an yi ma matsalar fyade rikon sakainar kashi. Ya ce “Idan mutum ya aikata fyade akan yarinya yar watanni shida da haihuwa, kama ta yayi a kashe wannan mutumen ba wai a daureshi ba. Yana ta faruwa a kasar nan kuma ba ayi ma masu laifin hukunci.”

Ya kara da cewa “Wai babu dokokin ne? Bamu da hukumomin da ke zartar da wadannan dokokin ne? Matsalar itace idana aka samu rahoton wadannan laifuffukan mutane basu daukarshi da mahimmanci.”

Da yake gabatar da kudirin tun farko, Oko ya bayyana cewa duk cikin yara 10 yan kasa da shekaru 18, to shida daga cikinsu na fuskantar masalar cin zarafin matantakarsu.

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel