Za a maido yan jihar Adamawa 4000 da sukayi gudun hijira zuwa kasar Kamaru

Za a maido yan jihar Adamawa 4000 da sukayi gudun hijira zuwa kasar Kamaru

-Za a maido da yan Najeriya yan asalin jihar Adamawa da sukayi gudun hijira zuwa kasar Kamaru

-Hajiya Sadiya Umar, komishinar hukumar kula da maido da yan gudun hijira ta kasa ce ta bayyana haka a lokacin da suka kaima gwamna Fintiri ziyara

-Fintiri ya bayyana cewa gwamnatinshi a shirye take wajen ganin ta tallafa ma yan gudun hijiran bayan an maido su

Kwamitin tsare tsare a kan maido da yan Najeriya dake Kamaru yace yan jihar Adamawa 4000 dake zaman gudun hijira a Kamaru za a maido su gida Najeriya.

Yan gudun hijiran sun gudu ne sakamakon tabarbarewar tsaro da akayi ta fama dashi a Najeriya musamman a arewa maso gabashin kasar.

A lokacin da yake karbar wakilan yan kwamitin a gidan gwamnatin jihar Adamawa dake a Yola, gwamna Ahmadu Umaru Finiri ya bayyana cewa gwamnatinshi a shirye take wajen ganin ta karbi yan gudun hijiran sun dawo gida lafiya.

Ya bayyana cewa gwamnatin a shirye take da ta taimaka wajen ganin an gudanar da aikin maido da yan gudun hijiran inda ya kara da cewa da zarar an maido su za kafa kwamiti da zai tallafa masu.

KARANTA WANNAN: Rikicin kabila: 'Karancin abinci ya mamaye jihar Taraba

Fintiri ya yabawa kwamitin da kuma hukumomin kasar Kamaru da suka daukin nauyin kula da yan gudun hijran.

Hajiya Sadiya Umaru Faruq, komishinar gwamnatin tarayya ta hukumar kula da yan gudun hijira ta kasa ta ce sun kai ma gwamna Fintiri ziyarar ne don su sanar dashi akan shirin da sukeyi na maido da ya gudun hijira yan asalin jihar Adamawa dake a Kamaru.

Hajiya Sadiya ta bayyana cewa za su fara aikin maido da yan gudun hijrar kwanannan sa’annan ta roki gwamnatin jihar da ta taimaka masu wajen ganin an gudanar da aikin cikin nasara.

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel