Wani mutum ya nemi kotu ta raba shi da masifaffiyar matarsa

Wani mutum ya nemi kotu ta raba shi da masifaffiyar matarsa

-Abin al'ajabi ya faru a jihar Ekiti inda wani mutum ya nemi kotu ta raba aurensa da matarsa

-Afolayan Babalola ya bayyana wa kotu cewa matar ta sa masifaffiyace kuma ta yawan fada da shi inda take cewa yana kula matan banza a waje

-Matar ta karyata gaba daya abinda mijin nata ya fadi a gaban kotun

Wani mutum mai shekaru 45, Afolayan Babalola a ranar Talata ya roki Kotun gargajiya ta Ado-Ekiti da ta raba aurensa da matarsa Adeyinka bayan sun kwashi shekara takwas tare a sanadiyar masifa da kuma rashin ganin mutuncinsa da bata yi.

Babalola wanda ke zaune a gida mai lamba 24 Covenant Avenue a birnin Ado-Ekiti ya fadi cewa, Adeyinka ta cika korafi, bata ganin mutuncinsa, kuma duk sanda za ta mashi magana tsawa take masa.

KU KARANTA:Mutumin da matarsa ta dabawa wuka ya samu lafiya, ya nunawa bidiyon tsairaci da matarsa ke tura wa samarinta

A cewar Babalola: “ Ta sha zargi na tare da yin fada da ni kan ina bin matan banza, ni kuma hakan ba dabi’ata bace. Ni Limamin coci ne ( Fasto), mutane na zuwa waje na neman addu’a. Mun dauki tsawon lokaci ba tare da mun kwana a daki daya ba, balle har maganar kusantar juna ta faru.”

Mijin ya kara da cewa zai dauki nauyin diyansu guda biyu idan har rabuwar ta su ta kasance. Inda ya fadi da bakinsa cewa zai rika basu naira dubu shida ko wane wata domin cin abinci.

A nata jawabin kuwa, matar, Adeyinka wadda ke zaune a Ajebandele cikin Ado-Ekiti ta karyata dukkanin abinda mijinta ya fadi.

Matar ta ce: “ Bana yi masa korafi, bana kuma yi masa tsawa, kai ni tsoronsa ma nake yi. Yana kira na da sunaye marasa dadi masu yawan gaske. Ba zan iya bar mashi yarana ba saboda shi din ba mutum bane mai zama a gida.”

Mai shari’ar kotun, Misis Olayinka Akomolede bayan ta saurari ta bakin ma’auratan biyu, ta dage karar zuwa 1 ga watan Agusta, 2019.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel