Zaben Kogi: Yan takarar APC 20 sun yi tawaye akan tsarin zaben fidda gwani

Zaben Kogi: Yan takarar APC 20 sun yi tawaye akan tsarin zaben fidda gwani

Yayinda ake ta shirye-shiryen zabe na jihar Kogi, mun samu labarin cewa Yan takarar zaben fidda-gwani na gwamnan jihar, a karkashin jam’iyyar APC, sun nuna adawa da tsarin zaben fidda gwanin da uwar jam’iyyar su ta kasa ta ce a gudanar a cikin sirri.

Yan takara sun sanar da hakan ne a cikin wata takadar korafi na rashin amanna da suka aika wa Shugaban Jam’iyyar na Kasa, Kwamrad Adams Oshiomhole.

Daya daga cikin yan takarar, Muhammed Aliyu ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Abuja a ranar Litinin, 8 ga watan Yuli.

A cewar Ali, sun je hedikwatar jam’iyyr ta kasa domin su jadadda rashin amincewar su da tsarin zaben fidda ’yan takara da APC ta ce a gunadar a cikin sirri a Kogi.

Za a gudanar da zaben gwamna a Kogi da Bayelsa ne a ranar 16 ga watan Nuwamba.

Idan za a tuna, ranar 5 ga watan Yuli ne uwar jam’iyyar APC ta bayyana cewa a yi zaben fidda gwanin takarar gwamnan Kogi a asirce.

Su kuma wadannan ‘yan takara su 20, suka fito a ranar 7 ga watan Yuli, suka taru, inda suka nuna rashin amincewar su da wannan umarni na uwar jam’iyyar APC.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Yan Shi’a da ke zanga-zanga sun harbi yan sanda 3 a majalisar dokoki

Daga nan sai suka kara cewa akwai makarkashiya a umarnin da uwar jam’iyya ta bayar domin a yi zabe a asirce, wanda suka tabbatar da cewa idan aka yi hakan, to abin da zai biyo baya ba zai yi wa jam’iyyar dadi ba.

A karshe sun ce ba za su tsaya su rike hannaye kawai, sun a kallo a tauye hakkin dimokradiyya a Jihar Kogi ba tare da sun yi magana ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel