Kotu za ta sanar da ranar yanke hukunci kan takardun shaidar sakandaren Buhari

Kotu za ta sanar da ranar yanke hukunci kan takardun shaidar sakandaren Buhari

Kotun daukaka kara da ke babbar birnin tarayya Abuja, ta bayyana cewa nan gaba za ta sanar da ranar da za ta yanke hukunci a kan karar da aka shigar game da sahihancin takardar shaidar kammala sakandare ta Shugaba Muhammadu Buhari, wadda ya yi amfani da ita wajen shiga takarar zaben 2019.

Kotun mai mambobi uku, karkashin jagorancin Mai Shari’a Atinuke Akomolafe-Wilson, bayan ta saurari bayanai daga masu shigar da kara da kuma bangaren wadanda ake karar, ta ce za ta bayyana musu ranar da za a yanke hukunci, da zaran kotun ta kammala komai.

A lokacin zaman kotun na ranar Litinin, 8 ga watan Yuli, lauyan masu shigar da kara, Ukpai Ukairo, ya dage a gaba masu shari’a cewa Buhari bai cancanci tsayawa takarar shugaban kasa ba, idan aka yi la’akari da takardun shaidar zurfin ilmin sa.

Lauyan ya ce dalili na farko shi ne, Buhari bai manna satifiket din sa na shaidar kammala sakandare ba a fam din INEC mai lamba CF001.

Lauyan ya kara da cewa tunda tilas doka ta ce sai da wancan fam din za a tantance dan takara, to Buhari bai gabatar da na sa fam din ba.

Sannan kuma ya kara jajircewa da cewa an shigar da karar a ranar 5 ga watan Nuwamba, watau a cikin kawanakin wa’adin kwana 14 da doka ta ce a daukaka kara.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Yan Shi’a da ke zanga-zanga sun harbi yan sanda 3 a majalisar dokoki

Ya ce shigar da karar ta su tun da farko ta samo asali ne tun daga ranar 25 ga watan Oktoba, 2018, ranar da INEC ta yi sanarwar wadanda suka cancanta tsayawa takara.

Daga nan sai ya roki kotu ta yanke hukunci ta hanyar wancakali da hukuncin Babbar Kotun Tarayya, wadda ta yanke cewa Buhari ya cancaci tsayawa takara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel